Connect with us

Wasanni

Arsenal da Manchester United na kan gaba na daukar Joao Felix

Published

on

Dan wasan gaba na Atletico Madrid Joao Felix, zai bar kungiyar ta Spain a watan Janairu.

Felix na shirin barin kungiyar ta La Liga a watan Janairu bayan ya kasa kafa kansa a bangaren Diego Simeone.

Atletico Madrid ta sayi dan wasan mai shekara 23 a kan Yuro miliyan 126 (£108m) daga Benfica a bazarar 2019. Amma wanda ya lashe gasar Euro 2016 bai iya daidaita salon da falsafar Simeone ba.

Yanzu dai Atletico ta shirya tsaf domin rage hasarar da take yi kuma ta rage farashin dan wasan inda ta nemi a ba ta aron fan miliyan takwas.

AS ta ruwaito Felix a shirye yake ya bar kungiyar a matsayin aro a wata mai zuwa inda Arsenal da Manchester United ke kan gaba wajen neman dan wasan na Portugal.

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.

Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.

Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Trending