Connect with us

Wasanni

Da Duminsa: Gakpo zai je Ingila domin sanya wa Liverpool riga

Published

on

Liverpool ta amince ta sayi dan wasan gaban Netherlands Cody Gakpo daga PSV Eindhoven.

Gakpo, mai shekaru 23, ya taka rawar gani a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar, inda ya zura kwallaye uku a ragar Netherlands a wasan daf da na kusa da karshe.

A na sa ran kudin dan wasan zai kasance tsakanin Yuro miliyan 40 zuwa 50 kwatankwacin Fam miliyan 35.4m zuwa 44.3m.

PSV ta ce, Gakpo zai tafi Ingila domin kammala cinikin, inda ta kara da cewa zai zama tarihi a gare su.

Liverpool ta fara zawarcin ‘yan wasan gaba wanada Luis Diaz da Diogo Jota suna fuskantar dogon lokaci a jinya.

Manchester United dai na zawarcin Gakpo.

“Hukumomin PSV sun kammala tattaunawar a ranar dambe kuma sun ba Gakpo izinin tafiya Ingila,” in ji wata sanarwa daga bangaren Eredivisie.

Gakpo dai ya taka rawar gani a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye tara kuma ya taimaka aka zura kwallaye 12 a wasanni 14 da ya buga wa PSV.

Ya kuma zura kwallaye uku sannan ya taimaka biyu a wasanni biyar na gasar Europa.

A gasar cin kofin duniya, ya zura kwallo a raga a duk wasannin da kasarsa ta buga da Senegal da Ecuador da Qatar.

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.

Continue Reading

Wasanni

Hukumar NPFL, ta amince da buƙatar Kano Pillars na ɗage wasan ta na mako na 28 da Enyimba

Published

on

Yanzu haka an samu dai-daito da hukumar NPFL, wanda ta amince da bukatar Kano Pillars na dage wasanta na mako na 28, da Enyimba zuwa ranar Alhamis, mai zuwa.

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ce ta wallafa hakan a shafin ta na Facebook da yammacin Litinin ɗin nan, ta ce ƴan wasan ta za su tashi a gobe Talata, da safe zuwa Aba domin fafata wasannin su.

Idan dai ba’a manta ba ƙungiyar ta wallafa kaɗan daga irin ƙalubalen da take fuskanta a harkokin gudanarwar ta.

Pillars, ta wallafa ƙalubalen ne kamar haka, “A yanzu haka zancan da muke muku Kano Pillars ta rasa kudin da za taje garin Aba, domin buga wasan hamayya na Nigeria Premier league wato Zobia Classic”.

Wasan dai shine wasa mafi ɗaukar hankali a league din Nigeria baki ɗaya, ku taya mu yadawa dan Allah.

Continue Reading

Wasanni

Glesner ya zama sabon mai horas da Palace.

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta sanar da nadin Oliver Glesner a matsayin sabon mai horaswar ta.

Glesner wanda tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ne mai shekaru 49 dan asalin kasar Austrian, ya maye gurbin tsohon mai horaswa Roy Hodson, wanda ake ganin ya gaza kai kungiyar ga tudun mun tsira.

A wasanni 16 da Crystal Palace ta buga a bayan nan ta yi rashin nasara a wasanni 10 duk karkashin jagorancin Roy Hodson wanda hakan yasa take mataki na 16 a teburin gasar firimiyar kasar Ingila.

Glesner dai ya rattaba kwantaragi da Palace har na tsawon shekaru biyu, zai kuma jagoranci kungiyar a wasan sa na farko da kungiyar kwallon kafa ta Burnley a ranar Asabar mai kamawa.

Continue Reading

Trending