Connect with us

Labarai

Mun kama miyagun kwayoyi na sama da Naira Bilyan 1 a shekarar 2022 – NDLEA

Published

on

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta bayyana cewar, ta kama miyagun kwayoyi na sama da Naira Bilyan daya da rabi a wannan shekarar da muke ban kwana da ita.

Shugaban hukumar a jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad ne, ya bayyana hakan a yayin zantawa da manema labarai a shelkwatar hukumar.

Yana mai cewar, suna samun goyon baya daga sarakuna da malamai da kuma kafafen yada labarai, kuma a cikin wannan shekarar sun gurfanar mutane 172 a kotu kuma tuni an hukunta 133.

Abubakar Idris Ahmad, ya kuma roki al’umma da a ci gaba da bawa hukumar bayanan sirri, domin dakile sha da fataucin miyagun kwayoyi a fadin jihar Kano

Labarai

Cutar mashako ta bulla a wasu sassan Jigawa

Published

on

Akalla mutum goma ne suka mutu bayan ɓarkewar cutar mashaƙo a kananan hukumomi 14 na jihar Jigawa.

 

Ma’aikatar Lafiyar jihar ce ta sanar wa manema labarai haka a Dutse, a yau Lahadi. Ta ce ana kuma zargin cewa mutum 91 sun kamu da cutar.

 

Babban sakatare a ma’aikatar, Dr Salisu, Mu’azu, ya ce zuwa yanzu, an tabbatar da mutum biyu da suka kamu da cutar a kananan hukumomin Kazaure da Jahun yayin da aka Ɗauki jinin wasu zuwa Abuja domin yin gwaji da tantancewa.

 

Mu’azu ya ce ɓarkewar cutar abin damuwa ne musamman ma ganin cewa ta ɓulla a yankunan da ba su taɓa yin riga-kafin ta ba.

 

A cewarsa, tuni ma’aikatar ta fara bincike domin tattaro bayanai daga yankunan da abin ya shafa.

 

Ya ce gwamnatin jihar tuni ta fara shiri don yin riga-kafi a yankunan domin kaucewa yaɗuwar cutar.

Continue Reading

Hangen Dala

Hukuncin kotu:- Zamu daukaka Kara – Abba Gida Gida

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zasu ɗauki matakin ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin tabbatar da adalci kan hukuncin da kotun sauraron korafe-korafen zabe ta yanke inda ta ayyana Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan da aka gabatar a watan Maris din 2023.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a daren laraba.

Gwamnan ya ƙara da cewa sun umarci lauyoyin su da su hanzarta wajen ɗaukaka ƙara ba tare da ɓata lokaci ba.

Ka zalika ya kuma ce wannan hukuncin bazai sanyar musu da gwiwa ba wajen ci gaba da gudanar da ayyukan da suka fara.

A ranar Laraba ne dai 20 ga watan Satumba 2023 kotun sauraron korafe-korafen zabe ta tabbatar da Nasiru Gawuna a matsayin Wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da aka gabatar a watan Maris. (more…)

Continue Reading

Hangen Dala

Hukuncin zaben Kano:- An Kori ‘yan Jarida daga harabar kotu

Published

on

Jami’an Ƴan Sanda sun hana ƴan Jarida shiga harabar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Kano.

Duk da asubanci da ƴan jarida suka yi, jami’an ƴan sanda sun yi ƙememe sun hana su shiga.

Ƴan sandan sun koro wakilan kafafen yaɗa labarai da dama zuwa can nesa da Kotun.

 

A yau ne dai za’a Yanke hukunci Kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.

 

Ƙarin bayani na tafe.

Continue Reading

Trending