Connect with us

Labarai

Kotu ta ƙara jaddada umarnin kamo tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso

Published

on

Babban kotun shari’ar musulunci dake zaman ta a Post office, karkashin mai shari’ah, Salisu Ibrahim Koki, ta kara jaddada umarnin ta na kamun tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso Kabiru Ado Panshekara. sakamakon karar sa da wani Dan kasuwa a jihar Kano Alhaji Auwalu ya yi.

Alhaji Auwal ya yi karar tsohon Chairman din kan zargin, ya sayar masa da wani katon fili da ake yin kamfani a ciki a yankin Challawa Naira 40 ba kadan, sai dai daga baya wanda aka siyarwar, ya gano akwai matsala akan fili, dan haka ya bukaci a dawo masa da kudin sa.

Tun da ya dawo da miliyan 20 sai yake ta yi masa jeka dawo akan sauran kudin, hakan tasa ya yi karar sa, kasancewar bai halarci zaman kotun ba, ta yi umarnin a kamo shi har sau biyu.

wakilin mu Abubakar Sabo, ya rawaito cewar, a zaman kotun na  ranar Laraba, lauyan tsohon shugaban karamar hukumar ta Kumbotso, ya roki kotun da ta je ta gano gidajen sa guda biyu daya Sharada, daya kuma a Kabuga housing estate, da kuma wata gona a Challawa, sannna a sa masa ranar biyan kudin idan bai biya ba a sayar da daya daga ciki tun da dukkan su sun kai kudin da ake bin sa, kuma ya roki kotun da ta janye umarnin kamun. Sai dai kotun ta amsa batun zuwa a ga wuraren amma ba ta amsa batun janye umarnin kamun ba.

Labarai

Iyaye ku dai ma marawa ƴaƴan ku baya akan abinda suke yi da ya saɓawa doka – Mai unguwar Ja’en Jigawa

Published

on

Mai unguwar Ja’en Jigawa da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano Sani Muhammad, ya ce bai kamata a rinƙa samun wasu iyaye da ɗabi’ar nan ta marawa ƴaƴan su baya akan abinda yaran suke aikatawa na saɓawa Doka, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Mai unguwar ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da gidan rediyon Dala FM, a lokacin da yake tsokaci kan yadda ake samun wasu daga cikin iyayen yankin sa na marawa ƴaƴan su baya kan abinda suke yi na ba dai dai ba, lamarin da yake ƙara ƙara kangarar da tarbiyyar ƴaƴan tare da tayar da hankalin al’umma.

Mai unguwa Sani Muhammad, ya kuma ce matuƙar yaran ba za su zauna lafiya a cikin unguwa da al’umma ba, to kuwa za su rinƙa ɗaukar matakin miƙa yaran hannun jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakin da ya dace a kan su, wajen ganin sun sauke nauyin da aka ɗora musu.

Sani Muhammad, ya ƙara da cewa ko a baya bayan nan wasu matasa sai da suka yi yunƙurin yin abinda bai kamata ba, lamarin da yasa aka ɗauki mataki a kansu amma aka samu wasu daga cikin iyaye suka marawa yaran nasu baya, wanda hakan kan haifar da barazanar tsaro.

Continue Reading

Labarai

Matasa ku ƙara dagewa da neman Ilmin addini da na zamani – Dr. Abdallah Gadan Kaya

Published

on

Fitaccen malamin addinin Musluncin nan Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci matasa da su ƙara mayar da hankali wajen neman ilmin addinin da na zamani, domin zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

Dakta Abdallah Gadan Ƙaya, ya bayyana hakan ne ta cikin Tafsirin Al-ƙur’ani mai girma, da yake gabatarwa cikin wannan watan azumin Ramadana a jihar Gombe.

A cewar sa, “Akwai buƙatar matasa ku yi riƙo da ƙananan sana’o’in dogaro da kai, da za ku rinƙa biyawa kan ku kuɗin makaranta wajen neman ilimi domin kaucewa zama a cikin jahilci, “in ji shi”.

Dakta Abdallah, ya kuma yi kira ga shugabanni da su dukkan abinda ya dace wajen inganta makarantu a sassan ƙasar nan, domin ganin ɗalibai sun samu ingantaccen Ilmi.

Continue Reading

Labarai

Za mu tsaurara matakan tsaro a lokacin bikin Sallah dan kare rayuka da dukiyoyin Al’umma – Daraktan gidan Zoo a Kano

Published

on

Hukumar kula da gidajen adana namun daji ta jihar Kano, ta ce, za ta tsaurara matakan tsaro a lokutan bukukuwan Sallah domin kare lafiya da rayuka, da kuma dukiyoyin Al’umma.

Manajan daraktan hukumar Alhaji Sadik Kura Muhammad, ne ya bayyana hakan da yammacin yau Litinin, a wani bangare na tunkarar bukukuwan ƙaramar Sallah, da ke tafe.

A cewar sa, “Mun gayyato jami’an tsaro daban-daban har da na fararen kaya da kuma jami’an hukumar Hisbah domin yaki da masu nuna rashin ɗa’a a bukukuwan Sallar, “in ji Kura Muhammad”.

Ya kuma ce, sun samar da karin sabbin dabbobin daji domim ilmantar da masu zuwa kallo musamman ma yara dalibai.

Wakiliyarmu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa, manajan daraktan Hukumar gidajen adana namun dajin na jihar Kano Alhaji Sadik Kura Muhammad, ya ƙara da cewa har yanzu ba su kara kudin shiga gidan Zoo ba, ga duk masu sha’awar zuwa kallo duk da cewa rayuwa ta kara tsada.

Continue Reading

Trending