Labarai
Tubabbun yan Boko Haram na gab da komawa wajen yan’uwansu – Irabor

Hukumomi a kasar nan sun kammala shirin miƙa wasu mayaƙan Boko Haram fiye da 600 da suka tuba ga gwamnatocin jihohinsu domin cigaba da sauran harkokinsu cikin Al’umma.
Hedikwatar tsaron kasar nan tace an ɗauki matakin ne bayan shigar da su cikin wani shirin gyara hali.
Hafsan hafsoshin kasar nan Janar Lucky Irabor ya tabbatar da kammala shirin miƙa tubabbun mayakan Boko Haram ɗin su 613 ga yan’uwansu.
Irabor Yayi wannan bayanin ne a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a ƙarƙashin tsarin nan na ba da damar miƙa wuya ko tuba ga mayaƙan Boko Haram, wato Operation Safe Corridor.
Ya ce, “zamu mika su ne ga jihohinsu na asali domin shigar da su cikin al`umma, kuma a halin da ake ciki ana gab da kammala aikin sauya musu tunani a cire musu tsohuwar akidar da suka dauko”. Inji Irabor
An yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan Boko Haram a Borno
Hafsan hafsoshin yace tubabbun mayakan Boko Haram ɗin na bukatar kulawa sosai a wannan gaɓa ta gyara hali da sake shiga cikin jama`a, don haka sai jihohin sun tsaya sosai a kan su’.

Labarai
Za mu ci gaba da karɓar tsofaffin kuɗi a Singa har nan da kwanaki 2 – Habibu Fantiya

Wani ɗan kasuwa dake kasuwar Singa a jihar Kano ya ce, Alhaji Habibu Yusuf Abdullahi Fantiyahar zuwa nan da kwanaki biyu za su ci gaba da karbar kudade a shagunansu, sai dai idan bankuna sun yi musu barazanar daina karbar tsofaffin kudi za su dakata.
Alhaji Habibu Yusuf Abdullahi Fantiya, ya bayyana hakan ne a zantawarsa da wakilin mu na ‘yan Zazu, Abubakar Sabo, yana mai cewar, al’umma daga garuruwa daban-daban sun shigo kasuwar, idan suka daina karɓar tsofaffin kuɗi za a cutar da su.
Akwai cikakken rahoton a muryar da ke kasa.

Labarai
Buhari zai tafi kasar Senegal

Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari zai tafi ƙasar Senegal ranar Talata domin halartar taron ƙasa da ƙasa kan harkokin noma karo na biyu da za a gudanar a birnin Dakar.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Femi Adesina ya fitar ranar Litinin.
Taron wanda shugaban Senegal kuma shugaban ƙungiyar ƙasashen Afirka ta AU, Macky Salla zai karɓi baƙunci – an shirya shi ne domin samar da kyakkyawan yanayin noma domin ciyar da haniyar Afirka.
Mista Adesina ya ce maharta taron za su tattauna batun shigar da abinci da sauran kayan amfanin gona zuwa wasu ƙasashen, ciki har da Najeriya.
Ya ƙara da cewa yayin da nahiyar Afirka ke da mutum miliyan 249 da ke cikin ƙagin yunwa, taron – wanda shugabannin ƙasashen Afirka da ministocin kuɗaɗen da na noma na nahiyar, da ƙungiyoyin duniya za su halarta – zai saka aniyar kawar da yunwa a nahiyar Afirka nan da shekarar 2030.
Daga cikin tawagar da za ta yi wa shugaba Buhari rakiya zuwa taron har da ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama, da ministan noma da raya karkara, Dakta Mohammad Mahmood Abubakar, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno da daraktan hukumar tattara bayanan sirri ta ƙasar Ambassada Ahmed Rufai Abubakar.

Labarai
Mun ƙara tsaurara matakan tsaro domin tunkarar zaɓen 2023 – NDLEA

A yayin da ya rage kwanaki 39 a fara fita babban zaɓen 2023 da ke ƙara gabatowa a ƙasa, hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Kano ta ce, yanzu haka ta ƙara tsaurara matakan tsaro a gurare daban-daban na Kano domin kawar da masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.
Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Idris Ahmad ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala a yau Litinin, inda ya ce shirin na hukumar ya shafi yayin da bayan zaɓen 2023 dake tafe.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su ƙara jan ƴaƴansu a jiki yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa don kaucewa faɗawarsu cikin mawuyacin hali.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, shugaban hukumar NDLEA ɗin na Kano Alhaji Abubakar Idris Ahmad, ya kuma ce yin amfani da miyagun kwayoyi ya kan sanya mutum yayi duk abinda ya wuce hankali bisa fita da suke yi daga hayyacinsu, a dan haka matasa su kaucewa sanya kan su a cikin harkokin shaye-shayen.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya8 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano