Connect with us

Labarai

Kurunkus: Ganduje ya rattaba hannu kan kudurin rarraba masarautar Kano

Published

on

Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar Karin sarakunan yanka guda hudu a Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano ce dai ta gabatar da kudurin dokar wanda ya kara Sarkin Bichi, da Sarkin Rano, da Sarkin Karaye da kuma Sarkin Gaya dukanninsu inda a baya suke karkashin ikon Mamartaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II wanda a yanzu ya koma Sarkin Birnin Kano.

Labarai

An tono wata gawa da aka bunne a Kano

Published

on

Tun da fari dai Babbar kotun shari’ar Muslunci ce mai zaman ta a  kofar Kudu ce karkashin mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, ta yi umarnin a yiwa gawar sutura kasancewar hukumar Hizba ta roki kutun ta yiwa asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano Umarnin su bayar da gawar wani mai suna, Abdullahi Obinwa, inda a nan ne aka samu akasi aka musanya gawar da ta wani dan kabilar Ibo mai suna Basil Ejensi, bayan kuma ya cika umarnin kotun da kwanaki bakwai da binne shi.

Sai dai wasu ‘yan kabilar Ibo suka garzaya kotun ta mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, suka yi roko a gaban kotun cewar anyi musu musayar gawa domin haka kotun ta yi umarni a kwakulo gawar da ta bayar da damar binewa kwani bakwai da suka gabata domin dai tasu ce bata wadanda suka nema ba tun da fari.

Bayan jin kowanne bangare mai shari’a Ustazu Ibrahim Sarki Yola, ya bayar da wani umarnin cewar a samu rakiyar jami’an tsaro zuwa makabartar domin tono gawar mai kwanaki bakwai a bunne ta a waccan makabartar ta unguwar Gandun Albasa dake Karamar Hukumar Birnin Kano, da yammacin ranar Litinin dinnan,

Harma bayan kwakulo gawar daga kabarinta ankuma damkata ga Lauyan gawar Masalinas Duru, harma lauyan ke cewa” Hukuncin kotun ya yi mana dadi sakamakon an bamu gawar mu”.

Shima limamin da ya sallaci gawar Malam Aminu Ahmad Adam, ya ce” Kuskure ne an riga an yi shi kuma babu wanda ya wuce ya aikata shi”.

Sai dai Jami’in hukumar Hizba mai lura da Makabarta, Malam Jamilu, wanda su ne suka yi kara ta farko ya ce” Na yi mamaki  game da wannan lamarin da ya kasance”.

Suma wasu da suka ganewa Idanuwansu yadda Ka hako gawar sunce har da jami’an tsaro a rakiyar kuma a gaban su aka kwakulo gawar sannan aka daura shi a gadon asibiti kuma tuni ‘yan uwan sa suka tafi da shi.

Continue Reading

Labarai

Muna dab da rufe rijistar baburan Adaidaita sawu -KAROTA

Published

on

Hukumar kula da zirga-zirgar ababan hawa ta jihar Kano, (KAROTA), ta ce za ta rufe yin aikin rijistar babura masu kafa uku wato adaidaita sahu a ranar Laraba mai zuwa.

Shugaban hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da ya yi da shugabannin kungiyar ‘yan Babura masu taya uku a yau Lititinin.

Ya ce” In Allah ya yarda a ranar Labara idan an rufe dole ne ya ajiye babur din sa sakamakon bas hi da lambar rijista a babur din sa saboda dazarar mun gan shi to ya karya doka”.

Ya kuma ce” Sannan ina sanar da masu baburan da su tabbata sun yi rijistar kafin ranar domin gudun haduwa damu ”. inji Baffa

Continue Reading

Labarai

Lassa na yi mana barazana inji jami’an lafiya       

Published

on

Shugaban kungiyar ma’aikatan lafiya da ungorzoma a jihar Kano, Ibrahim Muhammad ya ce cutar zazzabin lassa tafi barazana matuka ga rayuwar jami’an lafiya, matukar babu kayan aiki masu kariya ga jami’an a lokacin da su ke aikin kula da masu lalurar.

Ibrahim Muhammada ya bayyana hakanne a ganwarsa da gidan Radiyon Dala ta cikin shirin rahotanni daga ‘yan zazu na wannan rana.

Ya kuma ce,” cutar ta zazzabin Lassa cuta ce dake yaduwa daga wanda ya kamu zuwa ga sauran al’umma harma da jami’an lafiyar dake kula da me cutar matukar babu matakan kariya”.

Ya kuma kara da cewa” Akwai bukatar gwamnati ta samar da irin wadannan kayayyakin aiki a cibiyoyin lafiya, su kuma mutane su dauki matakan tsaftace muhalli domin kare kai daga kamuwa da cutar”.

Wakiliyar mu Hafsat Isma’il ta rawaito cewa, shugaban kungiyar ma’ikatan lafiyar ta kasa a jihar Kano, Ibrahim Muhammad, ya kuma jaddada muhimmancin matakan kariya, akan cutar ta zazzabin na Lassa.

 

Continue Reading

Trending

error: Content is protected !!
en_USEnglish
en_USEnglish