Connect with us

Addini

Abubuwan da ya kamata mu yi a lokacin da muke cikin fushi.

Published

on

Litattafan Addinin Musulunci
  • Fushi daga shaidan yake
  • Mu yawaita zama da Alwala da kuma ambaton Allah
  • Mu guji daukar hukunci lokacin da muke cikin fushi .

A shafin sa na facebook, Falalu Dorayi yayi tsokaci kan abubuwan dake jawo fushi, da kuma hanyoyi kauce musu kamar haka

Tasirin fushi a zucivar Dan Adam na iva haifar da masifu da abubuwa marasa dadi iri iri, ciki harda kisan kai.

Duk Lokacin da Dan Adam yake cikin fushi ko wani vanayi na bacin rai,Tabbas wannan mutumin na samun bakuncin Shaidan kusa da zuciyarsa, kuma duk hukuncin da zai yi a wannan lokacin ba zai zamo mai inganci ba,ma’ana zai dauki hukunci mara dadi.

Idan muka samu kanmu a irin wannan yanayin Ma’aiki Rasulullah (SAW) Ya bamu mafita:

  1. Mu daura Alwala
  2. Mu yawaita fadin “A’udhu billahi minashaytaan-ir-rajeem”
  3. Idan a tsaye muke mu zauna, idan bamu daina fushin ba kuma mu kwanta.

Kada mu biyewa zuciya, mu kasance masu  hakuri.

Rahoto: Koyi da halayen Annabi ne nuna tsantsar kaunar sa – Limamin Tukuntawa

Ubangiji  Yana son masu hadiye fushi da yafiya lokacin da aka fusata su.

Mu duba; (Ali Imran 3:134)

Allah Yasa mu dace

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending