Ƙasashen Ƙetare
Yadda birnin Makkah ya koma bayan saukar ruwan sama

. Yawan korayen ciyayi a birnin Makkah alama ce ta tashin alqiyama.
. Saukar ruwan sama ya sanya korayen ciyayi sun fito a birnin Makkah.
Shafin Haramain Sharifain ya wallafa cewa yanzu haka korayen ciyayi sun mamaye birnin Makkah sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.
Sai dai Malamai irin su Dakta Zakir Naik sunyi fashin baki, Ina suka ce hakan wata alama ce da take nuna kusantowar tashin alqiyama, dogaro da hadisin Annabi S.A.W,
“Alqiyama ba za ta tsaya ba har sai yankin larabawa ya koma kiwo da koramu, wanda hakan zai faru ne ta sanadin korayen ciyayi”. Muslim 157

Ƙasashen Ƙetare
Shek Shuraim yayi ritaya daga limancin Masallacin harami

Guda cikin manyan limaman masallaci Mai alfarma na Makkah Shek Shuraim ya rubuta takardar ajiye limancin masallacin.
Shafin Haramain Sharifain ya ruwaito cewa, cikin takarar ajiye limancin da Shek Shuraim ya rubuta, ya bayar da uzurin mayar da hankali kan wasu ayyuka da suka kulla yarjejeniya da shugabancin Kasar tun a shekarar bara ta 2022.
Sai dai takardar ta bayyana cewa, Shek Shuraim zai rinka zuwa masallacin domin jagorantar wasu salloli, musamman Tarawih a watan Ramadhana.
Shek Shuraim dai ya dauki tsawon shekaru Yana Jan sallah a masallacin harami, Kuma guda ne cikin gwanayen alqur’ani, inda wasu lokutan suke karanta shi da Shek Abdurrahman Assudais.

Ƙasashen Ƙetare
‘Yan Sanda sun ce Beraye ne suka shanye hodar Ibilis a ofishin su

‘Yan sandan kasar Indiya, sun ce ɓeraye sun lalata kusan kilogram 200 na hodar Ibilis da aka ƙwace a hannun wasu mutane da ke safararta aka kuma ajiye a ofishinsu.
“Ɓeraye kananan halittu ne da ba su san wani tsoron ‘yan sanda ba. Abu ne mai wahala iya kare su,” a cewar Kotu da ke zamanta a jihar Uttar Pradesh.
Kotun ta bukaci ‘yan sanda su gabatar da shaida da ke tabbatar da cewa ɓeraye ne suka lalata hodar.
Alkalin ya bada misali da kararraki uku da aka gabatar kan ɓeraye sun lalata kwayar.
Mai shari’a Sanjay Chaudhary ya ce ko a baya an samu rahotanni da ke cewa ɓerayen sun lalata kilo 195 na hodar iblis, da kuma kilo 700 duk a ofisoshin ‘yan sanda.
Sanjay ya faɗawa ‘yan sanda cewa ba su da kwarewar yaƙi da irin waɗannan ɓeraye. Ya ce hanya ɗaya tilo na kare aukuwar irin wannan shi ne kai hodar ko kwayar dakunan adana magunguna ko aiwatar da gwaji. In ji BBC.

Ƙasashen Ƙetare
Zaben Amurka: Zan sake tsaya wa takara a shekarar 2024 – Trump

Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin kasar a zaben 2024 na jam’iyyar Republican.
Trump na neman komawa fadar White House bayan da ya sha kaye a yunkurinsa na sake tsayawa takara a zaben 2020 ga Joe Biden.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jawabi a gidansa da ke Mar-a-Lago, Florida.
“Domin sake mayar da Amurka girma da daukaka. A daren yau ne nake sanar da cewa zan tsaya takarar shugabancin Amurka,” in ji Trump.
Ku tuna cewa Trump ya lashe zaben shugabancin Amurka a karon farko a shekarar 2016 lokacin da ya fafata da Hillary Clinton.
Trump zai zama shugaban kasa na biyu da zai sake karbar mulki a fadar White House idan ya yi nasara a shekarar 2024, inda ya zama shugaban kasa na 45 da na 47.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano