Connect with us

Manyan Labarai

CBN ya haramta bayar da sabbin kudi akan kanta

Published

on

  • CBN yayi umarni ga bankuna da su rinka zuba sabbin kudi a injin ATM
  • Bankuna na hada sabbi da tsofaffin kudade.

Babban Bankin Najeriya CBN ya haramta wa bankuna bai wa kwastomominsu sabbin takardun Naira a saman kanta.

Bankin yace maimakon haka, bankunan su tabbatar sun loda sabbin takardun kudin a injinan ATM don su wadatu a hannun ’yan Najeria kafin wa’adin 31 ga Janairu, 2023 da tsoffin takardun kudin za su daina aiki.

Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya na cewa,

CBN ya ba mu umarnin daina ba wa kwastomomi sabbin takardun N200 da N500 da kuma N1000 akan kanta.

“Maimakon haka, ya bukaci a loda kudin a wadace a injinan ATM don jama’a su samu su cire.”

“Nan take ake bukatar aiwatar da wannan umarni.”

Punch ta ce ta gano cewa CBN ya ba da umarnin ne ranar Laraba tare da bukatar a fara aiki da shi nan take.

Sai dai duk da haka, wasu bankuna sun ki bin umarnin na CBN sakamakon karancin sabbin tarkadun Naira, ballantana su su loda a ATM don amfanin jama’a.

A cewar majiyar, karancin sabbin takardun Naira ya tilastawa bankuna hada sabbi da tsoffin takardun N1,000 da N500 suna sakawa a ATM kafin lamurra su daidaita.

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya fara rusau

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta fara rushe wasu gine gine da aka yi su a wuraren gwamnati Ba bisa ka’ida ba.

A cikin daren Asabar din nan ne tawagar Kwamitin kar ta kwana mai lura da rushe gine gine ta fara da rushe wani sabon rukunin shaguna mai kunshe da sama da shaguna 90 dake jikin filin sukuwa a jihar Kano.

Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya bayyana cewar wannan aiki somin tabi ne domin batun rushe gine ginen da aka yi su akan filayen jama ar Kano lamari ne da babu gudu babu ja da baya kamar yadda gwamna Engr Abba Kabir Yusif ya bayyana a lokacin da yake yakin neman zabe.

Tawagar kwamitin na kar ta kwana zai cigaba da rushe dukkan wasu gine gine da aka yi su ba bisa kaida ba.

Continue Reading

Trending