Kimiya
SIKILA – Ko ka San matsalolin Ƙwayar Jini Mai Sikila?
Shafin Physiotherapy Hausa ya bayyana cewa Ciwon sikila ko kuma amosanin jini, wato ‘Sickle Cell Disease’ a turance, ciwon jar ƙwayar halittar jini ne da ake gadar sa daga iyaye (mace da namiji). Lafiyayyiyar jar ƙwayar jini tana da sifar da’ira ne. Amma masu ciwon sikila, jar ƙwayar jininsu tana zama sifar lauje ko baka ne, wato ‘sickle’ a turance.
A yayin da mafi yawan sifar jar ƙwayar jini ta zama sifar lauje a ciki jini:
1] Wannan zai rage wa jar ƙwayar jinin ikon shaƙar wadatacciyar iskar oksijin daga huhu domin kaiwa zuwa sassan jiki.
2] Saurin tafiyar ƙwayar jinin a cikin jijiyoyin jini zai ragu.
3] Harɗewa ko sarƙewar jajayen ƙwayoyin jini yayin da suke gogayya a ƙoƙarin shiga siraran jijiyoyin jini.
4] Fashewa ko mutuwar ƙwayoyin jini kafin cikar wa’adin kwanaki 115 zuwa 120 da ya kamata su yi suna aiki a jiki.
Daga cikin matsalolin da masu ciwon sikila ke fuskanta akwai:
1. ƙamfar jini, wato ƙarancin jini a jiki, sakamakon yawan fashewar ƙwayoyin jinin kafin cikar wa’adinsu.
2. Kumburin fuska, tafukan hannu da sawu.
3. Jinkirin girman jiki da tsaikon balaga.
2. Matsanancin ciwon jiki da gaɓɓai.
4. Sauri ko yawan harbuwa da ƙwayoyin cutuka da ke kama ƙashi da gaɓoɓi.
5. Lalacewar ƙashi da ruɓewar sassan jiki da dai sauransu.
Likitocin fisiyo na ba da gudunmowa ga masu ciwon sikila yayin da suka gamu da matsalolin da ke tattare da ciwon sikila kamar: matsanancin ciwon jiki da gaɓoɓi, riƙewar gaɓoɓi, raunin ko rashin ƙwarin tsokokin jiki, dashen gaɓar ƙugu, dashen gaɓar gwiwa, yanke sassan jiki, jinkirin matakan girman yaro da dai sauransu.
Muradin likitan fisiyo ga mai ciwon sikila shi ne samun rayuwa cike da aiki cikin kuzari da karsashi ba tare da ciwo ko nakasa ba.
MATAKIN KARIYA
Daga ƙarshe, ana iya kauce wa haɗarin haifar yaro mai ciwon sikila ta hanyar yin gwajin ‘genotype’ ga ma’aurata kafin aure domin gano yiwuwa ko akasin haifar yaro mai sikila.
Tabbata ka san gwajin ‘genotype’ ɗinka da na wace za ka aura domin tabbatar da cewa ba ku da haɗarin haifar yaro mai ciwon sikila.
Kimiya
Za a binne mai Otal ɗin Tahir a Kano Tahir Fadhallah
Shahararren ɗan kasuwar nan haifaffen jihar Kano, ɗan asalin ƙasar Lebanon, kuma Shugaban ƙungiyar Ƙwarori mazauna Najeriya, Alhaji Tahir Fadhallah Rasuwa.
Sanarwar da iyalan marigayin, Tahir Fadhallah, suka fitar ta ce, ya rasu a safiyar Juma’a a wani Asibiti a can ƙasar Lebanon, bayan ya sha fama da jinya.
Gawar Marigayin za ta iso Najeriya gobe Asabar da misalin karfe, wanda za a binne shi a Maƙabartar Kwarori dake nan Birnin Kano kan Titin sansanin Alhazai Hajj Camp.
Marigayi Alhaji Tahir Fadhallah, ya rasu ya na da shekaru 74, da ƴaƴa 5 da jikoki 10. A cikin ƴaƴansa akwai, Alhaji Muhammad Hammoud, shugaban rukunin kamfanonin Tahir.
Kimiya
Rahoto: Gwamnati ta duba mu wajen tsarin daukar ma’aikata – Masu hada magani
Ƙungiyar masu haɗa magunguna da fasaha ta ƙasa reshen jihar Kano (PHATAN), sun gudanar da taron ranar masu haɗa magunguna da Fasaha ta duniya, wanda su ka yi tattaki daga titin State Road zuwa Loadge Road, sannan su ka kai ziyara zuwa gidan marayu na Nasarawa da kuma gidan gyaran hali na Kurmawa.
Shugaban ƙungiyar, Kwamrade Isma’il Ado Dawakin Kudu, ya ce sun yi tattakin ne tare da baiwa gidan marayun da gidan gyaran halin magunguna.
Ga wakilin mu na ƴan Zazu, Tijjani Adamu.
Kimiya
‘Yan sandan Kano: Mun kama matashi da zargin haura gidajen mutane – DSP Kiyawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da nasarar cafke wani matashi da ya shafe sama da shekaru biyar, ya na haura cikin gidajen mutane, ya na sace musu wayoyin su na hannu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya bayyana hakan.
Ya ce “Yan sandan da ke yawon Sintiri ne a Rijiyar Lemo, su ka sami nasarar kama matashin, mai suna Abubakar Ibrahim, mai shekaru ashirin da biyar, mazaunin Unguwar Kurna”. Inji DSP Kiyawa.
Wata daga cikin wadanda matashin ya haura wa cikin gidajen su ya kwashe musu wayoyI, sun bayyana yadda wanda ake zargin ya raba su da wayoyin nasu har cikin gida.
Rundunar ‘yan sanda na kira ga mutane da su ci gaba da sanya idanu a cikin gidajen su, domin kawo karshen matsalar.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su