Manyan Labarai
Zaben 2023- jam’iyyar YPP ta mara baya ga jam’iyyar ADP.

. Yanzu jam’iyyar YPP ba ta da Dan takarar gwamnan Kano.
. Muna so a ciyar da matasan Kano gaba.
. Masu ruwa da tsakin jam’iyyar YPP sun mara baya ga jam’iyyar ADP.
Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar YPP Dakta Yakubu Uba Muhammad ya jingine takarar sa tare da mara baya ga Dan takarar gwamna na jam’iyyar ADP Hon Sha’aban Ibrahim sharada.
Cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun Hon shaaban sharada, Abbas Yusha’u Yusuf ya fitar ta ruwaito cewa Dakta Yakubu da mataimakin sa da kuma wasu daga cikin ‘Yan takarar kujerun majalisar tarayya dana jiha a jam’iyyar YPP sun mara baya ga jam’iyyar ADP me alamar littafi.
“Dakta Yakubu Uba ya sanar da Hon shaaban Ibrahim sharada cewa yanzu yayi watsi da takarar sa tare da mara baya gare shi, shi da dukkanin masu ruwa da tsakin jam’iyyar ta YPP a kano”.
” Babban abinda yasa Yakubu ya janye shi ne, domin a hada karfi da karfe wuri guda, domin ciyar da Kano gaba.” inji sanarwar.
Wannan dai na zuwa ne kasa da kwanaki hamsin a fara gudanar da babban zaben 2023.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Labarai
Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.
Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano