Connect with us

Manyan Labarai

Sabon rikici ya kara ruruwa a Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano

Published

on

Jam’iyyar PDP

Rikici ta ƙara ruruwa a jam’iyyar PDP na jihar Kano duk da hukuncin kotu na baya-bayan nan da kuma matakin ɗaukaka ƙara daga ɗaya bangaren.

Lamarin ya faru ne bayan tsagin Sadiq Wali wanda wata kotun tarayya ta shaida cewar ba shi bane ɗan takarar gwamnan jihar kano ba.

Hakan yasa ya kara ɗaukaka ƙara, daga baya kuma ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓensa a jihar.

BBC ta rawaito cewa a wannan Litinin ɗin ne ake sa ran kwamitin yaƙin neman zaben da ɓangaren Sadiq Wali suka ƙaddamar zai fara zama domin tattauna yadda zai gudanar da aikinsa.

A makon jiya ne aka kafa kwamitin, al’amarin da ya ƙara tayar da kura.

Ɓangaren Muhammad Abacha sun ce su basa tare da wannan matakin kamar, yadda Barrister Ibrahim Isa Wangida, lauyan jam’iyyar PDP a Kano ya shaida.

To sai dai bangaren Sadiq Wali wanda ya ƙaddamar da kwamtin ya ce, waɗanda suke sukar wannan matakin ba su fahimci yadda tsarin yake ba,a cewarkakinsu Dakta Yusuf Bello Danbatta.

Labarai

Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.

Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.

Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Published

on

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.

Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.

” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Published

on

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.

Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Continue Reading

Trending