Connect with us

Manyan Labarai

Zargin Badakala- kwamitin dattawan APC a karamar hukumar Fagge ya sauke Ali Baba

Published

on

Tambarin APC

kwamitin dattawan jam’iyyar APC na karamar hukumar Fagge ya bayyana dakatar da shugaban sa Hon Ali Baba Agama Lafiya Fagge sakamakon zargin sa da almundahana.

Cikin wata takarda Mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran Kungiyar na daya da na biyu, Hon Salisu Shitu da Hon Shehu Sani Chidozie ta bayyana cewa kwamitin dattawan na zargin Ali Baba da yin sama da fadi da wasu kudade da Kuma motocin da aka bashi ya rabawa ‘yan kwamitin.

A madadin dattawan jam’iyyar APC na karamar hukumar Fagge muna sanar da shugaban jam’iyyar APC na kano, shugaban Dattawa, Mai Girma Gwamnan Jihar kano, Dan takarar gwamnan kano, da mataimakin sa, cewa mun dakatar da shugaban kwamitin dattawan jam’iyyar APC na karamar hukumar Fagge daga shugabancin kwamitin sakamakon zargin sa da almundahanar kudade da motoci wadanda aka bashi ya rabawa kwamitin, wanda har yanzu ba’a bamu ba.” inji sanarwar.

Sai dai duk kokarin mu na jin ta Bakin Hon Ali Baba Agama Lafiya hakan mu bai cimma ruwa ba, da zarar mun same shi zamu martanin sa kan batun.

Hangen Dala

Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

 

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

 

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.

 

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

 

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Continue Reading

Hangen Dala

An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Published

on

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Continue Reading

Manyan Labarai

Hajiya Aisha Bura ta lashe zaben shugaban mata yan jarida na kasa NAWOJ

Published

on

Zaɓaɓɓiyar shugabar kungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta alkawarta yin tafiya da kowanne bangare domin samar da hadin kai da ci gaban mambobin kungiyar.

Hajiya Aisha Bura ta bayyana hakan jim kadan bayan kammala rantsar da ita a matsayin wadda ta samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a daren jiya.

Ta ce, akwai bukatar mambobin kungiyar su bata hadin kai don ganin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta samu nasara da kuri’u 498 yayin da abokiyar takarar ta kuma shugabar kungiyar mai barin gado Hajiya Ladi Bala ta samu kuri’u 381.


Continue Reading

Trending