Wasanni
Mai tsaron ragar kasar Faransa ya rataye takalmansa daga buga wasa – Hugo Lloris

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur Hugo Lloris yayi ritaya daga bugawa Kasarsa ta Faransa wasa, Lloris mai shekaru 36 ya bayyana hakanne makwanni uku da buga wasan karshe da kasar Faransa ta yi da Kasar Argentina a wasan karshe na gasar cin kofin duniya da kasar Qatar ta karbi bakwanci, inda kasar Faransar ta yi rashin nasara a wasan a bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Watanni biyu da rabi ya rage a fara buga wasan can canta na gasar cin kofin kasashen nahiyar turai.
Hugo Lloris wanda ya fara bugawa kasar Faransa wasa yana da shekaru 21 a duniya, a wasan sada zumunta da suka buga da kasar Uruguay a watan Nuwamban shekarar 2008, Lloris ya tallafawa kasar Faransa ta samu nasarori da dama wanda daga cikinsu har da nasarar lashe kofin duniya a shekarar 2018 wanda kasar Rasha ta karbi bakwanci,
Yayin zantawarsa da kafar French Publication L’Equipe yana mai cewa “Yanzu lokaci ya yi da ya kama ta na yi ritaya daga buga wa Kasa ta wasa, domin baiwa wasu dama, ya kama ta na baiwa Iyalai na lokaci na, sannan ina mika godiya bisa damar da a ka ba ni”. In ji Lloris.

Wasanni
Tsohon mai horas da Super Falcons Mabo ya rasu.

Tsohon mai horas da tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasa, Super Falcons, Ismaila Mabo, ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.
Dan uwansa Salisu Nakande Mamuwa ne ya bayyana rasuwar ta sa a shafin sa na sada zumunta a safiyar yau Litinin.
Karanta wannan labarin: http://flying eagles
Kafin rasuwarsa dai Ismaila Mabo ya jagoranci Super Falcons a gasar cin kofin duniya na mata, inda ya jagorance su zuwa wasan dab da na kusa da na karshe a shekarar 1999, ya kuma jagorance su zuwa gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da kuma 2004.

Wasanni
Silva ya tsawaita kwantaraginsa da Chelsea

Thiago Silva wanda ke buga wasa a baya, ya sake tsawaita kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na tsawon shekara daya, inda kwantaragin zai kare a shekarar 2024.
Silva mai shekaru 38, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga PSG ta kasar Faransa a shekarar 2020, kawo yanzu ya bugawa Chelsea wasanni 106.
Thiago Silva wanda dan asalin kasar Brazil ne, ya tallafawa Chelsea ta samu nasarori da dama wanda daga ciki harda nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Turai.

Wasanni
Za a iya Conte aikin gaggawa a mafutsara – Tottenham

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta baiwa mai horas da kungiyar, Antonio Conte, hutu yayin da a yau ake shirin yi masa aikin tiyatar gaggawa a mafutsararsa.
Kungiyar ta Tottenham ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta wallafa a shafin ta na internet.
Conte ya kamu da rashin lafiya a farkon wannan makon, kuma ya koka da matsanancin ciwon ciki.
An gano tsohon manajan na Chelsea ya na da cutar cholecystitis, yanayin da ke haifar da kumburi da ja na mafutsara.
Labarai mai alaka: Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal
Sanarwar ta Tottenham ta ce “A kwanan nan Antonio Conte ya yi rashin lafiya tare da matsanancin ciwon ciki.”
“Bayan an gano cutar cholecystitis, yau za a yi masa tiyata a mafitsara a yau, kuma zai dawo bayan wani lokaci idan ya samu murmurewa. Kowa a kungiyar ya na yi masa fatan alheri.” Inji Tottenham.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano