Manyan Labarai
Likitoci na barazanar tsunduma yajin aiki

Kungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta Najeriya ta yi barazanar tsunduma yajin aiki a faɗin kasar matuƙar gwamnatin tarayya ta gaza biya mata buƙatunta.
A wata wasiƙa mai ɗauke da sa-hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa Dakta Emeka Orji, da ƙungiyar ta aike wa ministan lafiya na ƙasar Dakta Osagie Ehanire, ta ce za ta fara yajin aikin matuƙar ba a magance musu matsalolinsu ba nan da ranar 24 ga watan Janairun da muke ciki.
Kungiyar ta ce watanni shida da suka gabata ta aika wa da gwamnatin tarayya gargaɗi game da wasu matsaloli da ta ce na shafar wasu mambobinta cikin har da batun kuɗin alawus na horaswa, da wasu alawus-alawus da ta ce tana bin gwamnatin tarayya na shekarar 2014, da 2015 da kuma 2016.
- Haka kuma ƙungiyar ta ce akwai wasu mambobinta da ke aiki a manyan makarantun lafiya na wasu jihohi da suka kwashe watanni ba tare da biyansu albashi ba.

Labarai
Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.
Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.
Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”
Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano