Connect with us

Manyan Labarai

Bamu da tunanin sauya jadawalin zabe – INEC

Published

on

Farfesa Mahmud Yakubu

Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmood Yakubu ya jaddada shirinsu na gudanar da babban zaɓen wannan shekara a lokacin da aka tsara, yana mai cewa “ba mu taɓa tunanin ɗage zaɓen ba”.

“Babban zaɓen 2023 zai gudana yadda muka tsara shi, duk wani rahoton da ya ruwaito saɓanin haka ba matsayarmu ba ce,” inji Yakubu.

Hukumar INEC ta tsara gudanar da zaɓen daga ranar 25 ga watan Fabarairu mai zuwa, inda za’a gudanar da zaben shugaban kasa dana sanatoci da ‘yan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, haka Kuma zaben Gwamna dana majalisun dokokin jihohi a ranar 12 Maris.

Sai dai yayin wani taro a farkon makon nan, wani babban jami’in INEC ya bayyana cewa idan ba a ɗauki matakan da suka dace ba matsalolin tsaro ka iya sanya ɗage zaɓen a wasu yankunan Najeriya.

Sai dai jawabin shugaban Hukumar Farfesa Mahmud Yakubu za’a iya cewa ya yanke duk wani shakku.

“Inec ba ta da wani tunanin sauya jadawalin zaɓen ballantana ma ɗage shi, Irin tabbacin da jami’an tsaro suka ba mu na tsaron lafiyar ma’aikatanmu ya ƙarfafa mana gwiwar ci gaba da shirye-shiryenmu”.

Manyan Labarai

Bama goyon bayan ƙirƙiro ƴan sandan jahohi dan ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a ƙasa – Human Rights

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Universal Declaration of Human Rights, ta ce akwai buƙatar duba na tsanaki gabanin sahale ƙirƙirar ƴan sandan jahohi, domin gujewa abinda ka je ya dawo.

Daraktan ƙungiyar a nan Kano Kwamared Umar Sani Galadanci, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da gidan rediyon Dala FM, a yau Talata.

Galadanci, ya kuma ce duba da a mafi yawan lokuta ake samun baragurbi a harkar samar da taro, kamata ya yi a wadata jami’an tsaron da ake da su da kayan aiki na zamani, ta yadda za’a ƙara musu Gwiwa akan aikin su.

“A ɓangaren ƙungiyar mu bama goyon bayan samar da ƴan sandan jahohi, domin hakan ka iya haifar da koma baya; kuma ba zai haifar da Ɗa mai ido ba a sassan ƙasar nan, “in ji shi”.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Umar Sani Galadanci, ya ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin tarayya da ta jahohi, su kula da al’ummar su tare da samar musu kayayyakin more rayuwa, dan rayuwar su ta tafi yadda ya kamata.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mutane uku sun rasu yayin ciro Waya a cikin Masai da ceto mutum ɗaya a Kano – Hukumar Kashe Gobara 

Published

on

Hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku, ciki har da Uba ɗan sa, a unguwar Ƴar Gwanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobarar PFS Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyanawa gidan rediyon Dala FM, faruwar lamarin a daren jiya Lahadi.

Tunda fari dai mutum na farko mai suna Mallam Ɗan Juma mai laƙabin Black, wayar sa ce ta faɗa a cikin Masai, ya shiga domin ya cirota, sai dai gaza fitowar sa ke da wuya sauran mutane ukun suka bishi domin ceto shi lamarin da suma suka gaza fitowa.

Sauran mutane ukun akwai ɗan mutumin mai suna Ibrahim Ɗan Juma mai shekaru 35, sai na ukun mai suna Aminu T Gaye, da na huɗu mai suna Abbas Alhassan, ɗan shekara 28, amma shi an ciroshi a raye.

PSF Saminu Yusuf, ya kuma ce bayan faruwar lamarin ne jami’an su, suka ceto mutum na ƙarshe a raye, amma ukun farko basa cikin hayyacin su baki daya.

Ya ƙara da cewa tuni jami’an nasu suka miƙa mutanen a hannun jami’in hukumar ƴan Sanda, kuma babban baturen ƴan sanda da ke ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano mai suna SP Ibrahim Lado, inda suka kai su asibitin ƙwararru na ƙaramar hukumar Tsanyawa a Kano.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gwamnan jihar Kano ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ƙasa ta Tal’udu

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ƙaddamar da fara aikin gadar sama da ta ƙasa da za’ayi a shataletalen Tal’udu, da ke ƙaramar hukumar Gwale, domin samar wa al’ummar jihar saukin zirga-zirga a yankin.

Gwamnan yanyi wannan jawabin ne da yammacin yau Asabar yayin da yake ƙaddamar da aikin.

Haka kuma gwamnan ya ce gwamnatin Kano za ta sanya idanu wajen ganin an kammala aikin cikin ƙanƙanin lokaci, hakan ya sa yanzu haka gwamnatin ta tanadi duk wasu kayan aiki da ake buƙata domin gudanar da aikin.

Har ila yau, gwamna Abba Kabir, ya ce yanzu haka gwamnatin sa ta shirya tsaf wajen bayar da tallafi ga matasa, domin samar musu da hanyoyin sana’o’in dogaro da kai.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙara da cewa an samo kamfani mai inganci wanda zai yi aikin cikin ƙanƙanin lokaci.

Continue Reading

Trending