Connect with us

Manyan Labarai

Za’a fara hako mai a jihar Nassarawa

Published

on

Kamfanin hakowa da sarrafa albarkatun man fetur na Najeriya NNPCL, yauwa bayyana cewa cikin watan Maris din 2023 ne za a fara aikin hako danyen man fetur a jihar Nassarawa.

Shugaban Kamfanin Mele Kyari ne ya bayyana hakan a shafin sa na Tuwita, inda ya ce “hakan ci gaba ne da aikin hakon mai da nufin samar da rijiyar mai ta farko a jihar”.

Ya shaida hakan a lokacin da yake karbar bakuncin tawagar fitattun yan asalin jihar ta Nassarawa, karkashin jagorancin Gwamnan jihar, Injiniya Abdullahi Sule a ofishin kamfanin da ke birnin tarayya Abuja.

Gano arzikin man a Nassarawa ya zo ne kusan wata biyar bayan da NNPC ya soma aikin hako mai a yankin Kolmani, da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.

Tun a shekarar 2019 ne kamfanin na NNPC ya bayyana gano albarkatun man fetur a yankin na Kolmani.

Kyari ya ce “binciken da aka gudanar ya nuna cewa akwai tabbacin kasancewar albarkatun ruwa mai yawa a jihar.”

Cikin wata sanarwa ta baya-bayan nan da NNPC ya fitar, Mele Kyari ya bayyana bukatar a hanzarta gudanar da aikin, ganin cewa karkatar da kasashen duniya suka yi zuwa ga makamashi ya janyo raguwar zuba jari a bangaren mai.

Ya kamata a gaggauta yin aikin saboda kasashen duniya na janyewa daga dogaro da man fetur, idan ba haka ba, shekaru 10 daga yanzu, babu wanda zai amince ya zuba kudi a kasuwancin man fetur.” kamar yadda sanarwar ta ambato shugaban NNPC na fadi.

A cewarsa, samun hadin kai daga al’umma da yanayi mai kyau na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar aikin, domin kaucewa irin barnar da yan bindiga ke yi wa bututan mai a yankin Neja Delta.

A martaninsa, Gwamna Sule ya taya mahukuntan kamfanin NNPC da gwamnatin tarayya murna, saboda kokarin da suka yi na ganin an soma aikin samar da mai a Kolmani da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar a Nuwambar 2022.

Hangen Dala

Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

 

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

 

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.

 

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

 

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Continue Reading

Hangen Dala

An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Published

on

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.

A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.

Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.

Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Continue Reading

Manyan Labarai

Hajiya Aisha Bura ta lashe zaben shugaban mata yan jarida na kasa NAWOJ

Published

on

Zaɓaɓɓiyar shugabar kungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta alkawarta yin tafiya da kowanne bangare domin samar da hadin kai da ci gaban mambobin kungiyar.

Hajiya Aisha Bura ta bayyana hakan jim kadan bayan kammala rantsar da ita a matsayin wadda ta samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a daren jiya.

Ta ce, akwai bukatar mambobin kungiyar su bata hadin kai don ganin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta samu nasara da kuri’u 498 yayin da abokiyar takarar ta kuma shugabar kungiyar mai barin gado Hajiya Ladi Bala ta samu kuri’u 381.


Continue Reading

Trending