Connect with us

Wasanni

Barcelona ta lashe super cup a karon farko bayan kwashe shekaru biyar

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta doke abokiyar hamayyarta ta Real Madrid a wasan karshe da suka buga a daren litinin da ci uku da daya, dan wasa Gavi ne ya fara zurawa Barcelona kwallo ta farko a minti na 33, sai dan wasa Robert Lewandowski ya zura kwallo ta biyu a minti na 45, daga bisani dan wasa Pedri ya kara tasa Barcelona gaba inda ya zura kwallo ta uku a minti na 69.

A bangaren kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid kuwa, dan wasa Karim Benzema ne ya zurawa Madrid kwallo daya a minti na 93, inda aka tashi wasan Real Madrid na da kwallo daya Barcelona na da kwallo uku, wanda hakan tasa Barcelona ta lashe kofin, rabon kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da kofin na super cup tun a shekarar 2018.

Wannan shine kofi na farko da Barcelona ta lashe karkashin jagorancin mai horaswa Xavi.

Labarai

Real Madrid ta kaddamar da Alexander

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta ƙaddamar da ɗan wasa Trent Alexander Arnold a yau a matsayin ɗan wasan ta

Inda shugaban ƙungiyar Flerontino Perez yace yau suna matuƙar Farin ciki kasancewar sun mallaki babban ɗan wasan baya a duniya.

 

Shima ɗan Wasa Arnold ya bayyana cewa yana cikin farin ciki kuma mafarkin sa ya cika na zama ɗan Wasan Madrid a yau.



Continue Reading

Labarai

Arsenal ba kanwar lasa ba ce – Me tsaron Gidan Real Madrid

Published

on

Me tsaron Gidan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Thibaut Courtois yace sun yi rashin nasara ne a wasan da suka buga a jiya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, saboda Arsenal din ba kanwar lasa ba ce.

A jiya Laraba ne dai aka fafata wasan kusa da na kusa da na karshe, tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Arsenal Inda Arsenal ta lallasa Real Madrid da ci 2 da 1.



Continue Reading

Wasanni

Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta 2023/2024.

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayer Leverkusen ta zama zakarar gasar Bundesliga ta shekarar 2023/2024, bayan da suka samu nasara a kan Weder Bremen da ci 5-0.

Hakan ne kuma ya kawo ƙarshen shekaru 11 da Bayern Munich, da ta yi tana lashe gasar.

Wannan dai shi ne karo na farko da Bayer Leverkusen suka taɓa lashe gasar a tarihi, ida suka gaza ɗaukar kofin a shekarar 2002 a ranar ƙarshe ta gasar.

Har ila yau, a dai wannan shekarar ne su kayi rashin nasara hannun Shalke 04, a wasan ƙarshe na German Cup Da ci 4-2.

Haka kuma, Real Madrid suka doke su a wasan ƙarshe na zakarun nahiyar turai.

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar bata taɓa ɗaukar wata gasa ba a ƙarni na 21, sai bayan da Xavi Alonso ya karɓe su.



Continue Reading

Trending