Connect with us

Wasanni

Kungiyar kwallon kafa ta Everton ta kori Lampard

Published

on

Tsohon da wasan kasar Ingila mai shekaru 44 Lampard ya karbi aikin horas da kungiyar kwallon kafa ta Everton a watan janairun shekarar 2022 da ta gaba ta, bayan sallamar mai horas da ita na wancan lokacin Rafael Benitez.

Everton dai ta yi rashin nasara a wasanni tara cikin wasanni 12 da ta buga a gasar Firimiyar kasar Ingila ta shekarar 2022 zuwa 2023 da muke ciki.

A ranar Asabar din da ta gabata dai kungiyar kwallon kafa ta Everton ta yi rashin nasara a karawar da ta yi da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United, wanda hakan yasa ta ke mataki na 19 da maki 15 a teburin gasar ta bana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Wasanni

Dembele ya tallafawa Barcelona ta kai wasan kusa da na karshe

Published

on

Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ousmane Dembele ne, ya zurawa Barcelona kwallo daya tilo a wasan kusa da na karshe da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Real Sociedad, a gasar Copa Del Rey da ke gudana a kasar ta Spain, wanda hakan ne yabawa Barcelona damar zuwa wasan kusa da na karshe a gasar.

Kawo yanzu, dan wasa Ousmane Dembele ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona kwallaye bakwai a kakar wasannin nan da muke ciki.

Continue Reading

Wasanni

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur ta sanar da daukan aron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Villarreal dan asalin kasar Netherlands wato Arnaut Danjuma mai shekaru 25 har zuwa karshen kakar nan da muke ciki.

Tun bayan da aka bude kasauwar saye da sayarwa na ‘yan wasanni a watan janairun nan da muke ciki, Arnaut Danjuma, shine dan wasa na farko da Tottenham Hotspur din ta dauka.

Tottenham Hotspur ta na mataki na biyar a teburin gasar firimiyar kasar Ingila ta shekarar 2022 zuwa 2023 da muke ciki.

Continue Reading

Wasanni

Memphis Depay ya koma kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta sanar da sayan dan wasa gaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dan asalin kasar Netherlands mai shekaru 28 Memphis Depay, akan kudi yuro miliyan uku, bi sa yar jejeniyar saka dan wasan gaban kungiyar Atletico Madrid Yannick Carrasco a cikin cinikayyar a nan gaba.

Depay wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona a shekarar 2021 daga kungiyar kwallon kafa ta Lyon, ya bugawa kungiyar kwallon kafa ta Barcelona wasanni hudu ne a wannan kakar da muke ciki ta shekarar 2022 zuwa 2023.

Ya kuma rattaba kwantaragin shekaru biyu da rabi da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid.

A baya bayan nan dai kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid ta bawa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea aron dan wasan su na gaba Joao Felix har zuwa karshen kakar nan da muke ciki.

Continue Reading

Trending