Manyan Labarai
Kano ta tsakiya= Abinda yasa har yanzu INEC ba ta sauya sunan Shekarau da Rufa’i Hanga ba – NNPP

Jam`iyyar NNPP, ta nuna damuwa game da kin amincewar da hukumar zabe ta yi da wasu sunayen da ta gabatar mata domin maye gurbin wasu daga cikin `yan takararta da suka janye.
Jam`iyyar ta ce ta kai maganar gaban alkali, kuma sau biyu kotu tana ba ta gaskiya, amma hukumar zaben ta ci gaba da yin turjiya.
NNPP, ta ce ta bi dukkan ka’idojin da doka da INEC ta shimfida wajen mika sunayen ‘yan takararta na mukamai daban-daban ciki har da kujerar sanatan Kano ta tsakiya, wadda tsohon gwamnan jihar sanata Ibrahim Shekarau, ya janye bayan ficewarsa daga jam’iyyar.
To amma, jam’iyyar ta fara zargin hukumar zabe nayi mata wasa da hankali har ma ta fara zargin ko akwai wata rufa-rufa da hukumar zaben keyi mata.
Injiniya Buba Galadima, jigo ne a jam’iyyar ta NNPP, ya shaida wa BBC cewa, su babban abin da ya dame su shi ne ko akwai wata jikakkiya tsakaninsu da hukumar zabe wadda ba su sani ba.
Ya ce, “ Duk dan Najeriya ya sani cewa Malam Ibrahim Shekarau, ya bar jam’iyyar NNPP, mun rubuta wa INEC cewa tun da Shekarau ya bar mu a bamu ranar da zamu sake zaben fitar da wani dan takarar da zai maye gurbin Shekarau.”
To amma sai INEC, ta rubuto cewa bata yarda ba, mu kuma muka fitar da dan takara muka aika musu amma suka ce ba su yarda ba,” inji shi.
Buba Galadima, ya ce daga nan suka garzaya zuwa kotu, kotu kuwa ta ce suna da gaskiya.
Ya ce, “Daga nan ne sai INEC, ta ce bata yarda ba ta daukaka kara, kotu ta gaba kuwa ta ce dole a kyale jam’iyyar da ya bari ta fitar da wani dan takara, sai suka ce sai sun sake daukaka kara zuwa kotun koli.”
Buba Galadima, ya ce ‘’ Wai shin mene ne ma bukatar INEC?”.
Bayan kujerar dan takarar sanata ta Kano ta tsakiya, akwai wasu kujerun kamar ta dan takarar sanata a jam’iyyar a Taraba ta Kudu Murtala Garba, wadanda a har yanzu hukumar zabe bata karbesu ba.
To sai dai kuma hukumar zaben ta ce bata da wata manufa game da jinkirin da ta ke yi wajen karbar sunayen masu takarar, face bukatar abi doka.
Wani babban lauyan a hukumar zaben, Tanimu Muhammad, ya shaida wa BBC cewa, ita hukumar zabe babu abin da take bukata illa kawai abi doka.
Ya ce,’’ Jam’iyyar NNPP ce ta fara gurfanar da mu gaban kotu, kuma ita kara a kan batun zabe karace da zata iya zuwa har kotun koli, shi ya sa muka tafi can don muna son sanin abin da ya kawo rikici tsakaninmu da ‘ya’yan jam’iyyar.”
Babban lauyan ya ce abin da suke nema su yi ya sabawa jadawalin da muka bayar.
Baya ga jam’iyyar NNPP, akwai wasu jam’iyyun da dama wadanda ke da irin wadannan korafi ko bukatar sauya sunayen da suke so su maye gurbin wasu ‘yan takara da suka janye, da suma suka zuba ido don ganin yadda zata kaya tsakanin hukumar zaben ta kasa da kuma jam’iyyar NNPP.

Manyan Labarai
An yi jana’izar Shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Ahmadu Haruna Zago

Ɗaruruwan mutane ne suka halarci sallar jana’izar shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna zago, wanda aka gudanar a kofar kudu a fadar mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu.
Babban kwamandan hukumar Hisbah na jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shine ya jagorancin sallar jana’izar a tsakar ranar Alhamis ɗin nan.
Daga cikin manyan manyan mutane da Suka hallarci sallar jana’izar marigayin Alhaji Ahmadu Haruna zago, akwai gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da tsohon kwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwakwanso, da mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, da sauran manyan mutane ciki har da masu riki da mukaman gwamiti.
Da safiyar Alhamis ɗin nan ne dai marigayi Ahmadu Zago, mai shekaru 74 ya rasu, a Asibitin Aminu Kano, bayan fama da rashin lafiya, kafin rasuwar sa yana da mata huɗu da ƴaƴa 37, da jikoki da dama.
Mai martaba sarkin kano Khalifa Muhammadu Sunusi na yayi addu’ar fatan Allah ya jikan marigayin ya kuma baiwa iyalansa da al’ummar jihar Kano jure rashin.
Tuni dai gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya miƙa saƙon ta’aziyyar sa ga al’ummar jihar da kuma iyalan marigayi Ahmadu Haruna Zago, tare da fatan Allah ya gafarta masa.

Manyan Labarai
Majalisar dokokin Kano ta amince da kafa rundunar tsaro mallakin jihar

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar kafa Rundunar tsaro mallakin gwamnatin jiha, bayan ɗaukar tsawon lokaci ana dambarwa a majalisar kan saɗarar dokar da ya ce ba’a yarda wanda yake riƙe da katin shaidar kowace jam’iyyar siyasa ba ya shugabanci rundunar tsaron.
Majalisar ta amince da samar da dokar ne bayan shafe kusan fiye da tsawon awa ɗaya ana muhawara akan da yawa daga cikin tanadin da dokar samar da rundunar tsaron ya yi kafin ayi mata karatu na uku.
Da yake ƙarin bayani akan kunshin dokar, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husani Dala, ya ce sun yi cikakken Nazari da hangen nesa kafin yin dokar wadda zata taba kowane bangare na jihar Kano wajen daukar ma’aikatan ta musamman wadanda basu da alaka da harkar siyasa.
“Dokar da muka samar ta amincewa jami’an rundunar tsaron ta jihar Kano da za a kafa su ɗauki kowane irin makami domin gudanar da ayyukan su, wanda ya haɗa da kamawa, hana aikata laifi da fatattakar masu aikata laifuka a fadin jihar Kano, “in ji Dala”.
Ditective Auwal Bala Durumin Iya guda daga cikin masana harkokin tsaro ne a ƙasar nan, ya ce akwai buƙatar abi ƙa’idoji wajen ɗaukar jami’an da za su gudanar da aikin rundunar tsaron da zarar gwamnan Kano ya sanya hannu a kan dokar.
A dai zaman na ranar Talata 04 ga watan Fabrairun 2025, majalisar dokokin Kano ta kuma amince da yin gyara akan dokar hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar nan, da hukumar da ke kula da sufuri a kwaryar birnin kano domin samun damar nada musu mataimaka.

Manyan Labarai
Za’a fara cin tarar Naira dubu 25 akan masu tofar da Yawu ko Majina, ko zubar da Shara ba bisa ƙa’ida ba a Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi dokar cin tarar Naira dubu 25 ga duk wanda aka kama da tofar da Yawu, da Majina, yin Bahaya ko zubar da Shara a sha tale-tale da kuma karkashin gadojin dake Kano.
Wannan ya biyo bayan dokar da majalisar ta Samar wadda za ta gudanar da ayyukan hukumar ƙawata birnin Kano da Kula da wuraren shaƙatawa.
Da yake Karin bayani ga manema labarai, Shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala, ya ce ya zama wajibi gwamnati ta dauki matakan da za su tsaftace Kano domin shigar da jihar sahun biranen duniya a fannin tsafta da cigaba.
“Bayan tarar ta Naira dubu 25, akwai kuma sauran hukunce-hukunce da dokar ta tanada wadanda za’ayi amfani dasu wajen ladabtar da duk wanda aka samu da laifukan, “in ji Lawan Dala”.
Majalisar ta kuma yi karatu na biyu kan gyaran dokar hukumar kwashe Shara da tsaftar Muhalli ta Kano domin Samar da mataimakin Shugaba.

-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su