Connect with us

Wasanni

Antonio ba zai bar kungiyar West Ham United ba a cewar Moyes

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United David Moyes ya ce, dan wasan gaban kungiyar mai shekaru 32 Michail Antonio ba zai bar kungiyar ba a wannan lokaci kamar yadda ake ta yada hakan a shafukan jaridu.

David Moyes ya bayyana hakanne a zantawarsa da manema labarai, inda ya kara da cewa, ko kadan kungiyar batayi yunkirin sayar da Antonio ba, “lokuta da dama dan wasan yakan so yayi abun da yake so, na tafiya ko akasin haka, amma har yanzu kungiya Hammer ta na bukatar Antonio, ta na bukatar salon yadda yake buga mata wasa” Ana ta alakanta dan wasan Antonio da kungiyoyi da dama.

Michail Antonio dai ya zurawa kungiyar kwallon kafa ta West Ham United kwallaye hudu ne a duka nin wasannin da ya buga mata a wannan kaka ta 2022 zuwa 2023 da muke ciki.

Wasanni

Tsohon mai horas da Super Falcons Mabo ya rasu.

Published

on

Tsohon mai horas da tawagar ‘yan wasan kwallon kafa ta mata ta kasa, Super Falcons, Ismaila Mabo, ya rasu ya na da shekaru 80 a duniya.

Dan uwansa Salisu Nakande Mamuwa ne ya bayyana rasuwar ta sa a shafin sa na sada zumunta a safiyar yau Litinin.

Karanta wannan labarin: http://flying eagles

Kafin rasuwarsa dai Ismaila Mabo ya jagoranci Super Falcons a gasar cin kofin duniya na mata, inda ya jagorance su zuwa wasan dab da na kusa da na karshe a shekarar 1999, ya kuma jagorance su zuwa gasar wasannin Olympics a shekarar 2000 da kuma 2004.

Continue Reading

Wasanni

Silva ya tsawaita kwantaraginsa da Chelsea

Published

on

Thiago Silva wanda ke buga wasa a baya, ya sake tsawaita kwantaraginsa da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na tsawon shekara daya, inda kwantaragin zai kare a shekarar 2024.

Silva mai shekaru 38, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Chelsea daga PSG ta kasar Faransa a shekarar 2020, kawo yanzu ya bugawa Chelsea wasanni 106.

Thiago Silva wanda dan asalin kasar Brazil ne, ya tallafawa Chelsea ta samu nasarori da dama wanda daga ciki harda nasarar lashe kofin zakarun nahiyar Turai.

Continue Reading

Wasanni

Za a iya Conte aikin gaggawa a mafutsara – Tottenham

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur, ta baiwa mai horas da kungiyar, Antonio Conte, hutu yayin da a yau ake shirin yi masa aikin tiyatar gaggawa a mafutsararsa.

Kungiyar ta Tottenham ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta wallafa a shafin ta na internet.

Conte ya kamu da rashin lafiya a farkon wannan makon, kuma ya koka da matsanancin ciwon ciki.

An gano tsohon manajan na Chelsea ya na da cutar cholecystitis, yanayin da ke haifar da kumburi da ja na mafutsara.

Labarai mai alaka: Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta dauki aron Danjuma daga Villarreal

Sanarwar ta Tottenham ta ce “A kwanan nan Antonio Conte ya yi rashin lafiya tare da matsanancin ciwon ciki.”

“Bayan an gano cutar cholecystitis, yau za a yi masa tiyata a mafitsara a yau, kuma zai dawo bayan wani lokaci idan ya samu murmurewa. Kowa a kungiyar ya na yi masa fatan alheri.” Inji Tottenham.

Continue Reading

Trending