Manyan Labarai
Kotun daukaka kara ta kori karar Muhammad Abacha tare da Ayyana Sadik Wali a matsayin dan takara

Kotun daukaka kara da ke zama a Kano ta soke hukuncin da babban kotu tayi wanda ta bayyana Muhammad Abacha a matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP kamar yadda jaridar Daily trust ta rawaito
Rahoto: Kotu ta ɗage shari’ar da Muhammad Abacha ke ƙarar INEC da PDP
Kotun daukaka karar ta yi umarnin cewa, Sadiq Wali, wanda a baya hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta ayyana shi a matsayin ‘dan takara, shi ne sahihin ‘dan takarar.

Hangen Dala
Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.
“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.
Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Hangen Dala
An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.
A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.
Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.
Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Manyan Labarai
Hajiya Aisha Bura ta lashe zaben shugaban mata yan jarida na kasa NAWOJ

Zaɓaɓɓiyar shugabar kungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta alkawarta yin tafiya da kowanne bangare domin samar da hadin kai da ci gaban mambobin kungiyar.
Hajiya Aisha Bura ta bayyana hakan jim kadan bayan kammala rantsar da ita a matsayin wadda ta samu nasarar lashe zaben da aka gudanar a daren jiya.
Ta ce, akwai bukatar mambobin kungiyar su bata hadin kai don ganin ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.
Hajiya Aisha Ibrahim Bura ta samu nasara da kuri’u 498 yayin da abokiyar takarar ta kuma shugabar kungiyar mai barin gado Hajiya Ladi Bala ta samu kuri’u 381.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano