Connect with us

Labarai

Kwalejin Sa’adatu Rimi: Za mu tabbatar sabbin ɗaliban digiri sun bi dokoki da ƙa’idoji – Farfesa Bunkure

Published

on

Shugaban Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke jihar Kano, Farfesa Yahaya Isah Bunkure, ya ce, sun yi taron sanar da sabbin ɗaliban digiri, dokoki da ka’idojin makarantar, domin ganin sun yi abinda ya dace, kamar sauran ɗaliban da suka kammala.

Farfesa Yahaya Isah Bunkure, ya bayyana hakan ne, yayin taron sanar da sabbin ɗaliban digiri, dokoki da ƙa’idoji makarantar, haɗin gwiwa da jami’ar Ahmadu Bello Zaria.

Muna da cikakken tattaunawar a muryar da ke kasa.

Labarai

Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.

Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.

Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Continue Reading

Labarai

Marayu na buƙatar tallafi sosai – Kwamared Abu Saleem

Published

on

Shugaban ƙungiyar tallafawa Marayu da ci gaban al’umma ta ƙaramar hukumar Birnin Kano Kwamared Adam Umar Abu Saleem, ya ce ƙarancin samun tallafi daga masu ƙarfi ne ke sanyawa Marayu ke faɗawa cikin mawuyacin hali.

Kwamared Adam Abu Saleem na wannan jawabin ne yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM, lokacin musabaƙar Alƙur’ani mai girma na marayu ƴan ƙaramar hukumar Birni 5 yayin da ɗalibi dake Karkasara Ja’afar Aliyu Abubakar ya zama gwarzon shekara na ƙaramar hukumar wanda aka ɗauki nauyin al’amuran rayuwarsa baya ga kyaututtuka da ya samu, wanda Musabaƙar ta gudana cikin Firamen Salanta a ranar Asabar.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa Kwamared Adam ya ce sukan shirya Musaɓakar ne domin zaburar da Marayu akan harkokin karatun Alkur’ani mai girma, da kuma rage musu wani tunanin maraici da suke kasancewa a maban-banta lokuta.

Continue Reading

Labarai

Lokacin zaɓe: Rundunar ƴan sanda ta shirya daƙile tayar da tarzoma – SP Kiyawa

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce, ta shirya wajen samar da tsaro, tare da ɗaukar matakin da ya dace ga ɓata garin da suke shirin tayar da tarzoma.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u a yau juma’a, yayin da yake tsokaci kan shirin da rundunar su ta yi kan zaɓe.

Continue Reading

Trending