Connect with us

Manyan Labarai

An girke jami’an yan sanda domin dakile zanga-zangar karancin naira da ake yi

Published

on

Babajide Sanwo-Olu

I’m An baza jami’an ƴan sanda a sassan birnin Jihar Lagos domin dakile tarzomar da ta ɓarke wadda ake kyautata zaton tana da nasaba da matsalar ƙarancin takardun kudin ƙasar na naira da ake fuskanta.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu manyan bankunan kasuwanci da ke Lagos sun ci gaba da kasancewa a rufe.

An riƙa jin ƙarar harbe-harben bindiga kuma an toshe manyan hanyoyi da dama inda wasu suka yi amfani da tayoyin da ke ci da wuta.

Ƴan sanda sun ce an dawo da doka da oda a gundumar Mile 12, sannan sun ɗora alhakin tashin hankalin a kan ɓata-gari.

Gwamnan jihar kaduna ya umarci yan jihar da su cigaba da amfani da Tsofaffin kudi

Jama’a na ci gaba da nuna bacin ransu a kan ƙarancin sababbin takardun kuɗin da aka sauya wa fasali, abin da ya haifar da zanga-zanga a farkon makon da ake ciki.

Manyan Labarai

Manufofin gwmanatin Tinubu na ƙuntatawa al’ummar ƙasa – Gamayyar ƙungiyoyin Arewa CNG

Published

on

Gamayyar ƙungiyoyin Arewacin Najeriya, CNG, ta bayyana fargabar ta kan taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasar, inda ta yi gargaɗin cewa salon lalube cikin duhu da gwamnatin tarayya ke yi na ƙara ta’azzara manyan ƙalubalen tattalin arziki ba tare da samar da wata ƙwaƙƙwarar mafita ba.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Jamilu Aliyu Charanchi, ya ce a halin da ake ciki kimanin ƴan Najeriya miliyan 133, ne ke fama da Fatara, yayin da aƙalla mutane miliyan 20 ke fama da rashin aikin yi a faɗin ƙasar.

Kwamared Jamilu Aliyu ya kuma soki manufofin gwamnati na taɓarɓarewar tattalin arziki, al’amarin da ke ƙuntata rayuwar ƴan Najeriya, kamar irin su hauhawar farashin kayayyaki da kuma ƙarin farashin man Fetur da kuma karin ƙudin wutar Lantarki.

A cewar sa, “Shugaban ƙasa Bola Tinubu akwai buƙatar ka rushe tawagar ka ta tattalin arziki domin sake fasaltawa, saboda ba su da zurfin fahimtar yanayin tattalin arzikin Najeriya a zahiri, “in ji shi”

Har ila yau, Kwamared Charanchi ya kuma ƙalubalanci duk wani yunkurin ƙara farashin man Fetur da sunan samar da kuɗaɗen aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata, inda ya bayar da shawarar a samar da wasu hanyoyin da za a bi wajen rage almubazzaranci da kuma tsadar tafiyar da gwamnati, domin samun sauƙi.

Kafar gidan rediyon Dala FM Kano, ta rawaito cewa, Kwamared Jamilu Aliyu ya kuma roki shugaba Tinubu da ya sa kishi da jajircewa wajen magance wahalhalun da al’ummar Najeriya ke ciki.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun shiga damuwa kan kwashe motocin da suke aikin hanyar mu – Mazauna garin Kara Gwarzo a Kano

Published

on

Al’ummar garin Kara da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano, sun jaddada rokon su kan magance musu matsalar rashin ruwan Sha da ta karancin Likitoci a asibitin yankin su, da ta lalacewar ajujuwa a makarantu, da kuma ta lalacewar hanyar su, al’amarin da ke damun su.

A zantawar wakilin Dala FM, Hassan Mamuda Ya’u da sakataren kungiyar Matasa ta samar da ci gaban garin na Kara da ke karamar hukumar Gwarzo, Khalid Sale, ya ce a baya-bayan nan gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya ƙaddamar da gyaran hanyar tasu, amma yanzu haka sun ga an kwashe motocin da suke aikin ba tare da sun san dalilin hakan ba.

Ya ci gaba da cewa, a don haka ne suke kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da dukkanin shugabannin yankin su, da su kai musu ɗaukin da ya dace dan magance musu matsalolin da suke addabar su.

“Tsayawar aikin gyara hanyar tamu da ta tashi daga bakin titin Gwarzo ta wuce zuwa unguwannin Kara, da Sabon layin Kara, ta wuce Ɗalangashi, har zuwa jihar Katsina, yanzu haka tayi matuƙar lalacewar da idan akayi ruwan sama muna shiga cikin Damuwa, “in ji Khalid”.

Ya kuma ƙara da cewa suna fama da matsalar rashin ruwan Sha, da ta ƙarancin Likitocin a Asibitin yankin su, da kuma ta lalacewar ajujuwa a makarantun su, amma ta lalacewar hanyar tafi yankin nasu tafi damun su.

A cewar sa, “Mun yi farin ciki da miƙa godiyar mu ga gwamnan Kano, bisa yadda ya ƙaddamar da gyara hanyar garin mu na Kara da ke ƙaramar hukumar Gwarzo, amma dai bamu ji daɗin kwashe motocin da akayi ba, domin yanzu haka aikin ya tsaya cak, “in ji shi”.

Akan al’amarin ne wakilin namu ya tuntubi shugaban riko na ƙaramar hukumar ta Gwarzo Mani Tsoho Zango, ta wayar tarho, sai dai a lokacin ya ce ya bashi lokaci kasancewar a lokacin da aka kirashin yana tsaka da wani uziri.

Idan ba’a manta ba al’ummar yankin sun daɗe da shaidawa Dala FM Kano, halin damuwar da suke cikin kan rashin al’amuran more rayuwa a yankin nasu.

Continue Reading

Manyan Labarai

Dalilan da suka sa bamu naɗa Sarki a Bichi ba – Gwmnatin Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce abin da ya sanya ba’a naɗa sarki a Bichi ba, saboda ba’a naɗa Hakimi a Bichi sai ɗan sarki, saboda tarihi da Bichi take da shi, a don haka yanzu Bichi ta na ƙarƙashin ikon cikin Birni, bisa yadda tarihin masarautar Kano take.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan jawabin ne da yammacin yau Juma’a, yayin taron ƴan jam’iyya da ya gudana a ɗakin taro na Afrika House da ke fadar gwamnatin jihar Kano, domin tattaunawa kan abubuwan da za su kawowa jam’iyyar su ta NNPP, ci gaba.

Gwamna Yusuf ya kuma tabbatar da cewa dukkanin sarakunan da aka naɗa, gwamnatin jihar za ta tabbatar ta basu haɗin kan da ya dace, domin ciyar da harkokin masarautun jihar gaba.

“Yanzu haka gwamnatin mu za ta fara shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar mu, “in ji gwamna Abba Kabir”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya alƙawarin taimakawa dukkannin ƴan jam’iyyar NNPP, maza da mata tun daga ƙasa, domin suma su tabbatar ana gudanar da mulki na gaskiya da riƙon amana dasu.

Continue Reading

Trending