Manyan Labarai
CBN ya umarci bankuna da su cigaba da karban tsofaffin 500 da 1000

Babban Bankin kasa,CBN ya umarci bankuna da su ci gaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗin naira 1,000 da 500 waɗanda yawansu bai zarta N500,000 ba.
Bankin na CBN ya bayyana hakanne a yau Juma’a, bayan koke-koken da ake ta samu a faɗin ƙasar kan wahalar da al’umma ke fuskanta wajen samun sababbin kuɗin.
Mai magana da yawun babban bankin, Osita Nwanisobi ne ya tabbatar wa BBC hakan.
Rahotanni daga wasu jihohin Najeriya dai sun bayyana cewa an gudanar da zanga-zanga kan ƙarancin sababbin kuɗin.
Kotu ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin daina amfani da tsaffin takardun kudi
An buƙaci jama’a su kai tsofaffin takardun kuɗinsu zuwa bankuna domin a musanya musu su da kwatankwacin kuɗin amma sababbi, sai dai tun gabanin wannan lokacin babban bankin kasa ya yi hani ga ‘yan Najeriya su riƙa cirar kuɗin da ya zarce naira 100,000 zuwa naira 500,000 a kowane mako ga kowane ɗan ƙasar ko ga kamfanoni.

Labarai
Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.
Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.
Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Manyan Labarai
Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.
Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.
” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”
Manyan Labarai
Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.
Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.
Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.
-
Nishadi3 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai3 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Nishadi3 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai2 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Lafiya10 months ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi3 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai3 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano