Connect with us

Manyan Labarai

An cire Naja’atu Muhammad daga harkokin kula da ‘yan sanda a lokacin zabe

Published

on

Hukumar lura da aikin ‘yan sanda ta kasa ta cire Hajiya Naja’atu Mohammed, daga matsayin ɗaya daga cikin masu sanya idanu na hukumar da za su lura da ayyukan ‘yan sanda a yankin arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce an janyo hankalinta ne kan wata sanarwa da jam’iyyar APC mai mulki ta fitar, inda ta yi zargin cewa Hajiya Naja’atu na goyon bayan wata jam’iyya don haka APCn take gani ba za ta yi wa jam’iyyar adalci ba.

A sanarwar da APCn ta fitar mai ɗauke da sa-hannun daraktan yaɗa labaran yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Jam’iyyar Festus Keyamo ya yi watsi da naɗin Hajiya Naja’atu a matsayin mai lura da ayyukan ‘yan sanda a lokutan zaɓen ƙasar.

Sanarwar da hukumar ‘yan sandan ta fitar ta ce ta maye gurbinta da tsohon mataimakin babban sifeton ‘yan sandan ƙasar Bawa Lawan domin lura da ayyukan ‘yan sanda a shiyyar ta arewa maso yamma.

Hukumar ta ce a koda yaushe tana taka-tsan-tsan a ayyukanta kuma za ta ci gaba da taimakawa wajen tabbatar da wanzuwar dimokradiyya a ƙasar.

Haka kuma ta sake jaddada ƙudurinta na tabbatar da samun sahihin zaɓe a ƙasar.

Labarai

Mu yawaita karanta Alƙur’ani da aikin alkhairi a watan Ramadan – Malam Ibrahim Bunkure

Published

on

Limamin masallaacin Juma’a na Salafussalih dake unguwar Ɗorayi ƙarama Malam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya shawarci al’ummar musulmi da su ƙara himma wajen karanta Al-ƙur’ani mai girma, tare da aikata ayyukan alkhairi domin rabauta da rahamar Allah S.W.T a nan duniya dama gobe ƙiyama.

Mallam Ibrahim Bunkure ya bayyana hakan ne lokacin da yake tsokaci kan huɗubar Juma’ar da ya gabatar yau a masallacin.

Ya ce, kamata yayi musulmai su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama, domin zama ababen koyi a rayuwa.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya kuma shawarci al’umma da su ƙara kasancewa masu yafiya musamman a lokacin da aka yi mutu abinda bai musu daɗi ba, bisa mahimmancin da hakan yake da shi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gawuna ya taya Abba Gida Gida murna

Published

on

Dan takarar Gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaben 2023 Dakta Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana karbar kaddara tun bayan da ya Fadi zaben 18 ga watan Maris.

Cikin Wani Sakon murya, Dakta Nasiru Gawuna ya godewa magoya baya, tare da yin fatan alkhairi ga sabuwar gwamnati.

” Wannan sabuwar gwamnati Allah ya Bata ikon yiwa al’umma adalchi, mu Kuma Allah ya bamu ikon yin biyayya.”

 

 

Continue Reading

Manyan Labarai

Abba Gida Gida ya karbi shaidar lashe zabe

Published

on

Sabon zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida gida ya karbi shaidar lashe zaben Gwamnan Kano.

Ya karbi wannan shaida ce yayin wani taro da hukumar INEC ta shirya domin bashi shaidar satifiket, bayan nasarar da ya samu a zaben ranar 18 ga watan Maris 2023.

Taron dai Wanda ya samu halartar da dama daga cikin manyan jihar Kano dama shiyyar arewa maso yamma, ya gudana ne a dakin taro na ofishin hukumar zabe INEC na jihar Kano.

Continue Reading

Trending