Connect with us

Labarai

Zaɓen Gwamna: Za mu kama duk wanda yayi yunƙurin tayar da hayaniya – DIG Hafiz

Published

on

Rundunar ƴan sandan kasar nan ta ce, za ta ɗauki matakin ba sani ba sabo, a kan duk wanda ta kama da yunƙurin tayar da hayaniya a lokacin zaɓen Gwamnoni da ƴan majalisu, a jihar Kano, wanda zai gudana a ranar Asabar mai zuwa.

Muƙaddashin babban Sifeton ƴan sanda na kasa, DIG Hafiz Muhammad Inuwa, wanda zai jagoranci aikin tsaron hukumar a nan Kano, yayin zaɓen Gwamnoni da yan majalisun jihohi ne, bayyaana hakan a zantawar da manema labarai a shalkwatar hukumar dake unguwar Bompai a jihar Kano.

Yace, hukumar za ta yi kasa a gwiwa ba wajan magance kowacce irin matsalar tsaro kafin lokacin zaɓen da ma bayan zaɓe.

Baba Suda

Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Published

on

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.

Cikakken labarin na Zuwa….



Continue Reading

Baba Suda

Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.

Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.

 

Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

 

 



Continue Reading

Baba Suda

NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Published

on

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.

 

Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.

 

A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.

Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.



Continue Reading

Trending