Labarai
Mu taimaka wa masu ƙaramin ƙarfi domin rage musu raɗaɗin rayuwa – Ambada Muhammad

Shugaban ƙungiyar mu haɗa zumunci ta KHZ Foundation dake nan Kano Ambasada Dakta Muhammad Abdulsalam, ya ce, taimakawa masu ƙaramin ƙarfi musamman a wannan lokaci na watan Azumin Ramadana, zai taimaka musu wajen rage musu wani raɗaɗin rayuwa na yau da kullum.
Ambasada Muhammad Abdulsalam ya bayyana hakan ne a yayin taron baiwa iyayen marayu da masu ƙaramin ƙarfi tallafin kayan abinci a ofishin kungiyar yau Litinin, da kuma basu a wasu unguwanni da suka haɗar da Tukuntawa da Sabuwar Gandu, Tinshama da dai sauransu.
Ya kuma ce, kamata yayi al’umma su ƙara himma wajen shiga makamancin ƙungiyar su domin baiwa al’umma gudunmawar da ta kamata, ta hanyoyi daban-daban, domin cire musu wata damuwa da ta damesu a rayuwa.
“Zamu fitar da ɗaurarru masu ƙananan tara a wasu gidjen ajiya da gyaran hali domin fitar da su daga halin rayuwar da suke ciki na jarrabta da suka tsinci kan su”. In ji Ambasada Muhammad.
Da yake nasa jawabin malami a kwalejin ilmin tarayya ta FCE dake nan Kano Mallam Ibrahim Muhammad Gandu, gargaɗar iyayen marayun da sukaci gajiyar tallafin yayi, da su yi amfani da kayayyakin abincin ta hanyar da ta dace Mai-makon siyar da kayan a ƙasƙance da ake zargin wasu suna yi a wasu lokutan.
Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, iyayen marayu da masu ƙaramin ƙarfi da dama ne suka rinƙa bayyana farin cikinsu, bisa basu kayan abincin da akayi, wanda suka haɗar da Shinkafa, Gero Taliya Man girki da sai sauransu, haɗi da Naira dubu ɗaya kuɗin Mota ga kowannen su.

Baba Suda
Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.
Cikakken labarin na Zuwa….
Baba Suda
Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.
Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.
Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.
Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.
-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su