Connect with us

Manyan Labarai

Zaben Kano – APC ta gabatar da bukatun ta gaban kotu

Published

on

Jam’iyyar APC reshen Kano ta shigar da kara a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan Kano, tana kalubalantar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) kan ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a jihar a ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A karar da jam’iyyar APC ta shigar da yammacin ranar Lahadin data gabata, APC na zargin cewa, Abba Kabir Yusuf bai cancanta ya tsaya takara ba, saboda ba ya cikin jerin sunayen mambobin NNPP da aka aika wa hukumar INEC.

Jam’iyyar APC ta kuma yi zargin cewa NNPP ba ta ci zabe da mafi yawan kuri’u na halal ba, tana mai cewa wasu kuri’un da aka kada musu na Jabu ne, kuma idan aka cire su daga kuri’un da NNPPn ta samu, APC ce za ta samu kuri’u ma fi yawa da aka kada.

APC ta kuma yi zargin cewa Baturen Zaben Gwamnan kano ya yi kuskure kan ayyana Abba Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ta ce tazarar kuri’un da aka samu bai wuce kuri’un da aka soke ba, kamar yadda ta bayyana cewa ya kamata a ce zaben bai kammala ba.

Kazalika APC na bukatar kotun da ta bayyana cewa NNPP ba ta da dan takara saboda Abba Kabir Yusuf baya cikin rajistar masu kada kuri’a da suka mika wa INEC a lokacin zabe, inda ya bukaci kotu ta bayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben, ko kuma ta bayyana APC a matsayin wadda ta lashe zaben da samun mafi yawan kuri’un da aka kada idan an cire kuri’un da APCn tayi zargin na bogi ne da aka kadawa NNPP.

Haka kuma mai shigar da kara ta roki Kotun da ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, yana mai zargin cewa tazarar ba ta kai adadin kuri’un da aka soke ba.

Tun abaya dai an jiyo jam’iyyar APC na kalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, inda tace za ta nemi hakkin ta a kotu.

Manyan Labarai

DSS sun kama Emefele bayan dakatar dashi daga Gwamnan banki

Published

on

Rahotanni na cewa jami’an tsaro na farin kaya DSS sunyi awon gaba da Godwin Emefele, sa’a guda bayan Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya dakatar dashi daga Gwamnan babban banki.

Tun abaya dai an zargi Emefele da hannu wajen gurgunta tattalin arzikin kasa, baya ga zargin sa, da hannu wajen tabarbarewar tsaro.

Continue Reading

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Gargadin Gwamnatin Kano Kan masu kaya a wuraren gwamnati

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi dukkanin masu kaya a wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta cefanar ba bisa ka’ida ba, dasu kwashe kayan su cikin gaggawa.

Cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ta fitar ta bayyana cewa, dukkanin masu kaya a shagunan da aka gina a jiki ko cikin makarantu, Maƙabartu, Asibitoci, Masallatai, gefen badala, Filayen ma’aikatu, Filayen wasanni da sauran wuraren shakatawa mallakin gwamnati da cewa suyi gaggawar kwashe dukkanin kayan su dake cikin shagunan da aka gina a waƴannan gurare ba tare da ɓata lokaci ba.

Continue Reading

Trending