Connect with us

Manyan Labarai

Da na hadu da kwankwaso da sai na mare shi – Ganduje

Published

on

Tsohon Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje yace da sun hadu da kwankwaso da akwai yiyuwar ya mare shi, a fadar shugaban kasa.

Tsohon Gwamnan ya bayyana Hakan ne yayin wata ganawa da gidan television na channels, yayin da yake martani Kan ganawar shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu da Kuma jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yammacin wannan juma’a.

” Nasan yana gidan Amma bamu hadu ba, da mun hadu akwai yiyuwar na kwada masa Mari” inji Ganduje.

Idan za’a iya tunawa dai kwanakin baya shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu yayi wata ganawa da kwankwaso, lamarin da aka jiyo tsohon Gwamnan na korafi cewa ba’a Yi musu adalchi ba, Koda dai a wancan lokaci, Ganduje ya musanta, ta bakin tsohon kwamishinan yada labarai Muhammad Garba, inda yace ba muryar Ganduje bace.

Wannan dai na zuwa ne a Gabar da gwamnatin Kano ke cigaba da rushe wuraren da tayi zargin gwamnatin baya ta Abdullahi Umar Ganduje ta cefanar ba bisa ka’ida ba.

Manyan Labarai

Tsadar Rayuwa: Zanga-zanga ba ita ce mafita ba a Najeriya – Sarkin Zazzau

Published

on

Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce tsadar rayuwar da aka samu kai yanzu a ciki zanga-zanga ba ita ce mafita ba, inda ya ce a guji yin irin abubuwan da ka iya haddasa kifar da gwamnatoci irin yadda ta faru a wasu kasashen Duniya.

Sarkin na Zazzau Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya bayyana hakan ne jim kadan da fitowar su daga ganawar da suka yi da shugaban kasa Tinubu, da ministoci da gwamnoni da kuma sarakunan gargajiya, a yammacin yau Alhamis.

Rahotanni dai sun bayyana cewa ganawar ta mayar da hankali ne akan hanyoyin daƙile zanga-zanga da kuma sauran matsalolin da ke addabar al’umma a ƙasa, da kuma samar da tsaro a kasa.

Dubban al’ummar ƙasa ne dai suka ƙudiri aniyar gudanar da zanga-zanga akan tsadar rayuwar da aka samu kai a ciki, wanda suka bayyana ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta mai kamawa, domin gudanar da zanga-zangar, don nusartar da gwamnati halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa, kamar yadda kafar Dala FM Kano ta rawaito.

Har ila yau, Sarkin na Zazzau a wata tattaunawar sa da kafar yada labarai ta DW, ya ce duk abinda kwanciyar hankali bai kawo ba, babu makawa tashin hankali ba zai kawo ba, a don haka akwai bukatar al’umma suyi hakuri tare da bin hanyoyin da suka dace mai-makon yin zanga-zangar.

Alhaji Nuhu Bamalli, ya ƙara da cewa, ya kamata gwamnati ta tabbatar da tsaro ta yadda za’a samu zaman lafiya a kasa, wanda al’umma za su koma gona domin ci gaba da aikin noman su mai-makon a rinka basu tallafin da ba zai iya magance musu talaucin da suke ciki ba.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mafi ƙarancin albashi N70,000 ya shafi Direbobi, Masu Gadi, da masu aikin Gida – Cewar Akpabio shugaban Majalisar Dattawa

Published

on

Majalisar Dattawa ta ƙasa, ta ce duk ma’aikatan gwamnati, da ma waɗanda ba na gwamnatin ba, irin su masu gadi, da Direbobi, da kuma masu Shara da wanke-wanke, duk sun shiga cikin sahun karɓar mafi ƙarancin albashin Naira 70,000, a Najeriya.

Shugaban majalisar dattawan Sanata Gidswill Akpabio, ne ya bayyana haka ne a zaman majalisar da aka yi na ranar Talata, bayan da majalisar ta amince da sabon ƙudirin biyan mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a Najeriya.

Akpabio, ya kuma ce idan mutum Tela ne kuma ya ɗauki ma’aikata, to ya sani ba zai biya shi ƙasa da Naira 70,000 ba, kuma idan uwa ce mai jariri kuma tana son ɗaukar ƴar aikin gida don kula da yaron, itama zata biya ta dai-dai da mafi ƙarancin albashin da aka amince da shi, kuma dokar ta shafi kowa da kowa.

A cewar sa, “Idan ka ɗauki direba ko mai gadi ba za ka biya su kasa da N70,000 ba, a don haka, na yi matuƙar farin ciki da aka ƙaddamar da haka, kuma a yanzu muna sa ran masu ɗaukan ma’aikata su inganta kan abin da aka kafa kowa ya bi, “in ji Akpabio”.

Har ila yau, shugaban majalisar dattawan, ya kuma taya ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa, da ma ɗaukacin ƴan Nijeriya, da majalisar Dokoki ta ƙasa, murnar wannan doka da aka kafa, wanda har ma aka rage wa’adin tattaunawar daga shekaru biyar zuwa shekaru uku.

Ya ce duba da yadda tsadar rayuwa ke ci gaba wannan kuma wani muhimmiyar doka ce, a don haka yake taya kowa murna akan ta.

A makon da akayi bankwana da shi ne dai Dala FM Kano, ta kawo muku labarin yadda shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu, ya amince da mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70,000, ga ma’aikata a Najeriya, al’amarin da suma ƙungiyoyin ƙwadago suka yi maraba da batun.

Continue Reading

Manyan Labarai

Na yi takaici kan rashin kulawa da makarantar Governors College – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koka tare da nuna takaicinsa bisa yadda ya sami makarantar Governors College, cikin rashin kulawa, da yadda ɗaliban makarantar suke karatu babu abubuwan zama, da yadda wasu ajujuwan suke cike da ruwa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan jawabin da yammacin yau, yayin wata ziyarar bazata da ya kai makarantar, domin ganin yadda aikin ta yake gudana, da kuma tabbatar da anyi mata aiki yadda gwamnati ta tsara.

Gwamna Abba Kabir, ya kuma ƙara da cewa, ya yi tsammanin yadda makarantar take ta waje fesfes a waje, hakan ma zai ga cikin ta amma sai ya tarar da saɓanin hakan.

“Muna kira ga manyan ƴan kasuwa da suke faɗin jihar Kano da su shigo domin tallafa wa harkar ilimi musamman makarantun firamare da na sakandire, domin ciyar dasu gaba, “in ji Abba Kabir”.

Idan ba’a manta ba, Tun a baya Dala FM Kano, ta kawo muku labarin yadda gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya dokar ta ɓaci akan Ilmi a jihar.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da magance duk wata matsala da ta shafi fannin ilimi a faɗin jihar Kano.

Continue Reading

Trending