Manyan Labarai
Abinda ECOWAS ta cimma a zaman ta na alhamis
Shugabannin ƙasashen yammacin Afrika ECOWAS sun bayar da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar su ɗaura ɗamarar kai yaƙi Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.
Sanarwar da guda cikin shugabancin ECOWAS Omar Aliu Toure, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen a kan Nijar.
Sun cimma wannan matsaya ce yayin taron gaggawa da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja.
Tun da farko, Ecowas ta baiwa sojojin da suka yi juyin mulki wa’adin kwana bakwai don su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed da suka hamɓarar daga mulki, ko su fuskanci matakin amfani da ƙarfin soji.
Shugabannin sun ce sun yi nazari kan rahotannin jakadun da suka aika da kuma muhawara cikin tsanaki a kan shawarwarin da manyan hafsoshin tsaron Ecowas suka bayar da kuma sauran bayanan da hukumar ƙungiyar ƙasashen ta gabatar.
Sun kuma nanata Allah-wadai da juyin mulkin Nijar da kuma ci gaba da tsare Shugaba Bazoum Mohamed.
Manyan Labarai
Tirƙashi: Wasu Matasa sun bankawa Dai-dai ta Sahu wuta a Kano
An yi zargin wasu fusatattun matasa sun bankawa wani baburin Adai-daita Sahu Wuta, tare da yunƙurin saɓawa masu baburin kamanni, domin huce haushin su akan su.
Tunda fari dai an zargi masu baburin ɗan sahun (keke Napep) da satar dabbobin mutane a Maƙabartar unguwar Maikalwa da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, lamarin da fusattun matasan suka ɗauki mummunan matakin akan su.
Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa wakilinmu Nasir Khalid Abubakar cewar, an ƙona baburin ne a yammacin Asabar, tare da yunƙurin far wa masu babur ɗin daga bisani jami’an tsaro suka kai ɗauki tare da tafiya da matasan da ake zargi da satar dabbobin.
Wakilin tashar Dala FM Kano, ya ruwaito cewa, bayan faruwar lamarin ne kuma wasu matasa a yankin suka yi ƙoƙarin kashe wutar da ke ci a baburin Adai-dai Sahun, da zummar idan ta mutu su ɗebi kayayyakin da basu ƙone ba a matsayin Ganima, sai dai jami’an ƴan sanda suka tarwatsa su.
Akan batun mu so jin ta ɓangaren rundunar ƴan sandan jihar Kano, sai dai haƙar mu bata cimma ruwa ba, amma za aji mu da ita da zarar ta magantu.
Manyan Labarai
Kitumurmurar da gwamnatin Tinubu take shiryawa jihar mu ba za ta yi tasiri ba – Gwamantin Kano
Gwamnatin jihar Kano ta ce babu wata matsalar tsaro a ko kuma shirin tayar da hargitsi a jihar, da aka rinƙa yadawa cewar za a iya samu a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar cikin daren juma’ar nan ta 24 ga watan Janairun 2025.
Ya ce rahotannin da ake yaɗawa cewar za a iya samun tayar da hargitsi daga wasu ƴan ta’adda a jihar, gwamnatin jihar Kano bata da masaniya akan batun, kuma lamarin bashi da tushe ballantana makama.
“An zo an jibge jami’an tsaron ƴan sandan gwamnatin tarayya a mashigar filin wasa na Sani Abacha Stadium, da sunan za a hana Maulidin da aka saba gabatarwa duk shekara, wanda aka shirya gudanarwar a gobe Asabar, inda jami’an tsaron ke neman hanawa, kuma ba zamu mu amince da hakan ba, “in ji Waiya”.
A cewar sa, Kitumurmurar da gwamnatin shugaba Bola Tinubu take shiryawa jihar Kano ba za ta yi tasiri ba.
Wanan dai na zuwa ne bayan da rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta bakin kakakin ta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta sanar da cewar, ta samu bayanan sirri kan yadda wasu ɓata gari ke shirin tarayyar da tarzoma jihar Kano, al’amarin da gwamantin jihar ta musanta.
Manyan Labarai
Mun samu bayanan sirri kan ƴan ta’addan da ke shirin tayar da hankali jama’a a Kano – Jami’an Tsaro
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ta shirya tsaf haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro domin daƙile ayyukan wasu ɓata gari da ta samu rahoton sirri akan su da suke shirin tayar da hankalin jama’a a jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani saƙon murya da ya aikowa Dala FM a ranar Juma’a 24 ga watan Janairun 2025.
SP Kiyawa, ya ce akwai buƙatar al’umma su ƙara sanya idanu a unguwanni su da ma wuraren harkokin su na yau da kullum tare a sanin mutanen da ke shiga cikin su, don taimaka wa wajen magance matsalar tsaron.
“Ga dukkanin wanda ya ga faruwar wani baƙon al’amari zai iya sanar da ofishin ƴan sanda mafi kusa don ɗaukar matakin da ya dace cikin gaggawa, ko kuma ya kira waɗannan lambobin wayar 08032419754, ko 09029292926, ko kuma 08123821575, “in ji SP Kiyawa”.
Har ila yau, Kiyawa ya ce Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano CP Salman Dogo Garba, tuni ya bada umarni aka baza jami’an taron ƴan sanda domin samar da tsaro a faɗin jihar Kano, tare da daƙile ayyukan ɓata garin.
-
Nishadi5 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su