Connect with us

Hangen Dala

Korar kwankwaso :- Rikici na cigaba da dabaibaye jam’iyyar NNPP

Published

on

A talatar nan ne dai Kwamitin Amintattu na jam’iyyar NNPP ya bayyana dakatar da jagoranta Sanata Rabiu Musa kwankwaso, sakamakon zargin sa da yiwa jam’iyyar zagon kasa.

Jim kadan bayan wata ganawa da kwamitin yayi, sakataren kwamitin Babayo Muhammad Abdullahi yace sun dauki matakin dakatarwar ne sakamakon zargin Sanata kwankwaso da yiwa jam’iyyar zagon kasa, da suka hadar da hada kai da wasu jam’iyyu na daban, PDP da Labour party, sai Kuma jam’iyyar APC da Kuma shugaban kasa Bola Tinubu.

Wanda dukkanin wadannan abubuwa sun saba da kundin tsarin tafikar da jam’iyyar NNPP.

Sai dai Kuma wannan na zuwa ne a gabar da wani tsagi a jam’iyyar ke cewa har yanzu Sanata kwankwaso yana nan a jam’iyyar.

Da yake zantawa da tashar talbijin ta Channels TV da yammacin Talatar nan, sakataren kwamitin amintattu na jam’iyyar, Mallam Buba Galadima ya yi watsi da rahotannin cewa wasu jiga-jigai a NNPP sun dakatar da Rabi’u Kwankwaso tsawon wata shida.

Ya ce mutanen sun gudanar da taron ne a daidai lokacin da kwamitin zartarwa na ƙasa a NNPP ke tabbatar da matakin korar da aka rigaya aka yi musu.

Wata ƙungiya ce a ƙarƙashin jagorancin wasu ƙusoshin NNPP, Mista Boniface Aniebonam da Agbo Major suka bayyana matakin dakatar da Kwankwaso bayan wani babban taro na musamman a birnin Ikko cikin jihar Lagos.

Haka zalika sun sanar da dakatar da kwamitin zartarwar NNPP na ƙasa.

Rahotanni sun ce ƙungiyar na cewa “ƙwararan shaidu” da suka bayyana sun tabbatar da cewa Kwankwaso na da hannu dumu-dumu a “wasu harkoki na yi wa jam’iyyar zagon ƙasa yayin taruka daban-daban”.

Sun ce matakin dakatarwar ya zo bayan binciken da wani kwamitin ladabtarwa ya yi.

Sai dai, ɓangaren Kwankwaso ya ce mutanen da suka yi dakatarwa tuni da ma an riga an kore su daga jam’iyyar NNPP.

Haka Kuma jam’iyyar NNPP a Kano tace ba ta san da waccar dakatarwa ba, hasalima ta gudanar da taron Kara mara baya ga Sanata kwankwaso a matsayin jagoran jam’iyyar, kamar yadda shugaban jam’iyyar NNPP na Kano Hashimu Suleman Dungurawa ya shaida mana.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Trending