Connect with us

Hangen Dala

Majalisa ta dakatar da Shugaban karamar hukumar Gwale

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso na tsawon watanni uku.

Majalisar ta ɗauki matakin ne a zamanta na yau Talata bayan samunsa da laifin sayar da wuraren gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.

Majalisar ta kuma ce ta same shi da laifin rashin gudanar da aiki da majalisar kansilolin karamar hukumar da sauran wasu laifukan.

Hakan ya biyo bayan rahoton bincike kan ƙofin da aka gabatar wa majalisar a kansa.

Majalisar ta kuma sanar da maye gurbin Khalid Ishaq Diso da mataimakinsa tsahon watanni uku har sai an kammala bincike.

A ganawarsa da manema labarai, shugaban kwamitin harkokin Ƙananan hukumomi da masarautu kuma ɗan kuma wakilin Sumaila a zauren Alhaji Zubairu Hamza Massu, ya bayyana rahoton da kwamitin nasu ya gabatar.

Hangen Dala

Jami’ar Chikago ta baiwa Atiku bayanan Tinubu

Published

on

Jami’ar Jihar Chicago da ke Amurka ta saki takardun karatun Shugaba Bola Tinubu, bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar a a 2023 ƙarƙashin jam’iyyar PDP Atiku Abubukar ya buƙaci hakan.

 

A ƙarshen makon da ya gabata ne, wata kotun gunduma da ke arewacin Illinois a Amurka ta bayar da umarnin a sakarwa Atiku takardun karatun Tinubu.

 

A wani martani na buƙatar da Atiku ya miƙa a karo na uku, wanda ya nemi a saki kwafin sakamakon digiri 1977, Jami’ar ta ce takardun sun yi daidai da na Tinubu da ke ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Yunin 1977.

“Bayan bincike mai zurfi, Jami’ar CSU ta gano ta kuma gabatar da takardun da aka nema kuma ta gabatar da su don amsa wannan bukatar. Lambobin takardun su CSUO008 zuwa CSU0010.

 

“An shafe sunayen ɗaliban da ke kan takardun saboda a sakaya sunansu.

“CSU za ta kuma saki sakamakon daliban da suke kusa da shi, masu lamba CSU0011 da lamba 0017 na wasu ɗaliban bayan an doɗe sunayen (saboda a sakaye sunanyensu)”.

 

“Waɗannan takardun sun yi daidai da yadda na Tinubu, dalibin da aka yi wa sauyin makaranta yake,” kamar yadda jami’ar ta rubuta.

 

A baya Tinubu ya yi iƙirarin ɓatan ainihin takardunsa na jami’ar, abin da ya sa ya gabatarwa da hukumar zaɓe INEC wata takardar a matsayin madadin takardun na ainihi domin takarar shugabancin Najeriya a 2023.

 

Takardu da dama na waɗari a kafafen sada zumunta a matsayin shaidar kammala karatun na Tinubu a Jami’ar jihar Chicago.

 

Tambari da kuma bajon da jami’ar CSU ta saki na digirin a 1977 sun yi daidai da irin wanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC, sai dai an samu banbanci a kwanan wata.

 

Sai dai cikin bayanin da jami’ar ta yi, ta ɗauki alhakin kuskuren da aka samu a kwanan watan, tana cewa kuskure aka samu wajen rubutawa.

 

A ranar 19 ga watan Satumba ne, Jeffrey Gilbert na kotun majitare da ke Amurka ya amince da buƙatar da aka shigabar gaban kotun tare da ba da umarnin sakin takardun karatun Bola Tinubu cikin sa’a 24.

 

A wani ƙoƙari na ganin haka bai faru ba, Tinubu ya ɗaukaka ƙara kan wannan umarni.

Nancy Maldonado ta kotun tarayya ta sake tabbatar da wannan hukunci da Tinubu ya so ƙalubalanta, inda ita ma ta ce a saki takardun.

 

Domin bin umarnin kotun da cika buƙatar Atiku Abubakar CSU ta ce ba za ta iya nemo ainihin kwafin takardun da ta bai wa Tinubu ba 1979.

 

“A tsarin CSU ba ta ajiye kwafin takardun ɗaliban da suka yi digiri, kuma bayan dogon bincike ta gaza samo kwafin irin wanda ta bau wa Tinubu a 1979, don haka ba a samu takardun da aka buƙata ba,” in ji jami’ar.

 

Sai dai jami’ar ta saki takardun wasu ɗaliban da ta rufe sunayensu, waɗanda suka yi daidai da na Tinubu domin tabbatar da cewa ya kammala makarantar a baya.

 

Atiku Abubakar dai na son amfani da takardun ne a matsayin shaida a kotun ƙolin Najeriya kan ƙorafin da ya shigar game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da aka yi a 2023.

BBC

Continue Reading

Hangen Dala

Hukuncin Kaduna :- PDP za ta daukaka kara

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ta tabbatar da zaben Gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC, inda ta ce za ta garzaya kotun daukaka kara.

Alberah Catoh, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Juma’a a Kaduna.

Catoh ya ce, wani nazari da lauyan PDP ya yi ya nuna cewa hukuncin bai cika wasu ka’idoji na tabbatar adalci ba.

Martanin ya zo ne sa’o’i bayan kotun da ke zamanta a Kaduna ta amince da nasarar zaben Sani.

Ya kara da cewa hukuncin bai dace da wasu dokoki da ka’idojin zabe ba.

Sanarwar ta kara da cewa, “Saboda haka jam’iyyar ta umurci lauyoyinta da su daukaka kara kan hukuncin da aka yanke a kotun daukaka kara da ke Abuja a cikin wa’adin da doka ta kayyade.”

Catoh ya kuma bukaci magoya bayan jam’iyyar PDP a fadin jihar da su kwantar da hankalinsu tare da nuna kwarin gwiwarsu kan lamarin.

Continue Reading

Hangen Dala

Abba ya biyawa Daliban Kano kudin makaranta

Published

on

Abba Kabir ya biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero

 

Gwamnatin jihar Kano ta ce, ta biya kuɗin makarantar ɗaliban Jami’ar Bayero, waɗanda ba su samu damar biya ba, kimanin Naira Miliyan ɗari bakwai.

 

Sakataren hukumar bayar da tallafin ilimi ta jihar Kano, Hon. Kabir Getso Haruna ne, ya bayyana hakan a ranar Talata.

 

Yana mai cewa, “Yanzu haka Gwamnatin Kano, ta biya wa ɗalibai ƴan asalin jihar, dubu bakwai kuɗin makarantar”.

 

Ya kuma ce, “Daga yau Talata, dukkan ɗaliban, su tafi Jami’ar Bayero, tsangayoyin su, domin ƙarasa rijista na shekarar 2023, su ci gaba da karatu”. Inji Hon. Kabir Getso.

Continue Reading

Trending