Connect with us

Labarai

Za mu daƙile tayar da hargitsi yayin yanke hukuncin zaɓen gwamna- Civil Defence

Published

on

Rundunar tsaro da bayar da kariya ga al’umma ta Civil Defence da ke jihar Kano, ta ce, za ta gudanar da aikin ba sani ba sabo a kan dukkanin waɗanda suka nemi tayar da hargitsi a gobe Laraba, yayin yanke hukuncin zaɓen gwamna a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar DSC Ibrahim Idris Abdullahi ne, ya bayyana hakan, yayin zantawarsa da gidan rediyon Dala FM a ranar Laraba, lokacin da yake tsokaci kan haɗin kan da za su yi da sauran rukunin jami’an tsaro kan tsaron da za su bayar yayin yanke hukuncin da Kotun karɓar ƙorafe-korafen zaɓen gwamna za tayi a gobe Laraba.

Ya ce, “Ba za su saurarawa duk wanda ya nemi tayar da hargitsin ba”.

Wakilnmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewar, DSC Ibrahim Idris ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, da su ka haɗar da masu riƙe da masarautun gargajiya, malamai da sauransu da su ci gaba da wayar da kan mutane domin ganin an samu zaman lafiya da cigaba.

Labarai

Za’a fara yiwa ɗalibai gwajin Ƙwaya kafin su shiga kwaleji a Kano

Published

on

Kwalejin fasaha ta jihar Kano, Poly Technic, za ta fara gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban da za su nemi gurbin karatu a shekara mai zuwa ta 2025.

Shugaban kwalejin Dakta Abubakar Umar Faruk, ne ya bayyana hakan yau Asabar, a yayin taron wayar da kan ɗalibai illar Shan miyagun ƙwayoyi domin kare kai daga cin zarafin Jinsi, da ƙungiyar ɗaliban kwalejin ta shirya.

Taron ya gudana ne a ɗakin taro na Farfesa Hafiz Abubakar, da ke reshen kwalejin na matan fada, da ke jihar Kano.

Shugaban kwalejin wanda maga-takardar makarantar Muhktar Ibrahim Bello, ya wakilta, ya ƙara da cewar matakin gwajin ta’ammali da miyagun ƙwayoyin hakan zai taimaka wajen yaƙi da miyagun kwayoyi a kwalejin da ma jihar Kano.

Da yake na sa jawabin akan dabarun kaucewa Shaye-shaye kwamandan hukumar NDLEA ta ƙasa reshen jihar Kano, Abubakar Idris Ahmad, wanda mataimakiyar sa Hajjiya Aisha Hamidu,ta wakilta, ya ce ta hanyar wayar da kai ne ɗalibai da matasa za su gane illar amfani da miyagun ƙwayoyi.

A nasa ɓangaren shugaban kungiyar ɗaliban ƴan asaln jihar Kano, da suka shirya taron Abdurrazak Nasiru Ahali, ya ce sun shirya taron ne domin wayar da kan ɗalibai akan illar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, ta yadda za su kaucewa amfani da su.

Taron faɗakar da ɗaliban illar miyagun kwayoyin yasamu halartar malamai,masu rike da sarautar gargajiya da sauran masana a fannin Ilimi da lafiya.

Continue Reading

Labarai

Mun ƙaddamar da kwamitin karta-kwana da zai kawo ƙarshen cutttuka masu yaɗuwa a Kano – Abba Kabir Yusuf

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da kwamitin kar-ta kwana da zai dunga shiga lungu da saƙo na jihar, domin yin riga-kafin cututtuka don kare jihar daga barazanar kamuwa da cutuka masu yaɗuwa.

Kwamitin dai an kafashi ne ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda zai jagoranta.

Da yake ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa kwamitin da aka ƙaddamar zai gudanar da aikin sa ne yadda ya kamata, ta yadda za’a dunga shiga lungu da saƙo na jihar domin magance duk wasu cututtuka masu yaɗuwa a faɗin jihar.

“Muna kuma kira ga dukkanin waɗanda aka naɗa a wannan Kwamitin da su tabbatar da cewa sun gudanar da aikin su yadda ya kamata wajen riƙe gaskiya da amana, “in ji gwamnan”.

Da yake jawabi a matsayin shugaban kwamitin mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar wa da gwamnan cewa za su gudanar da aikin su yadda ya kamata domin ciyar da Kano gaba da kare ta daga barazanar cututtuka masu yaɗuwa.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, an samarwa da kwamitin baburan hawa guda 88 inda aka karrama masu maganin gargajiya da lambar girmamawa yayin taron ƙaddamar da kwamitin.

Continue Reading

Labarai

An gurfanar da matasan da ake zargi da sace bindiga AK-47 a Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gurfanar da waɗanda ake zargi sace bindiga kirar AK-47, a Kotu, yayin zanga-zanga.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya sanar da hakan a shafin sa na sada zumunta, ya ce an gurfanar dasu a gaban kotu, yau Litinin a kotu mai lamba 54 da ke Nomand-sland a jihar Kano.

Continue Reading

Trending