Hangen Dala
Hukuncin zaben Kano:- An Kori ‘yan Jarida daga harabar kotu

Jami’an Ƴan Sanda sun hana ƴan Jarida shiga harabar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe ta Kano.
Duk da asubanci da ƴan jarida suka yi, jami’an ƴan sanda sun yi ƙememe sun hana su shiga.
Ƴan sandan sun koro wakilan kafafen yaɗa labarai da dama zuwa can nesa da Kotun.
A yau ne dai za’a Yanke hukunci Kan karar da jam’iyyar APC ta shigar gaban kotun tana kalubalantar nasarar Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Ƙarin bayani na tafe.

Hangen Dala
Zargin Almundahana:- An kama jami’in gwamnatin Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.
Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajiyar da ke Sharada.
“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.
Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike .

Hangen Dala
An yiwa kasafin Kudin 2024 karatu na biyu

Majalisar Dattawan Najeriya da ta Wakilai sun yi wa kasafin kuɗin ƙasar na 2024 karatu na biyu ranar Juma’a kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya gabatar musu da shi.
A ranar Laraba ne Tinubu ya je majalisar tare da gabatar da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin abin da gwamnatinsa za ta kashe a 2024, kuma ya nemi ‘yan majalisar su gaggauta amincewa da shi.
Sai dai shugaban bai bayyana adadin abin da kowace ma’aikata da hukumomin gwamnati za su samu ba a lokacin da ya yi gabatarwar, abin da ya jawo cecekuce da muhawara a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ‘yan majalisar na kokawa yayin muhawarar da suka yi ranar Juma’a game da ƙarancin bayanai kan kasafin, wanda suka ce ya sa sun mayar da hankali ne kawai kan abubuwan da Tinubu ya faɗa a jawabinsa.
Jam’iyyun adawa sun soki kasafin da cewa “na yaudara ne”, yayin da Shugaba Tinubu ya yi masa laƙabi da “kasafin sabunta fata”.

Hangen Dala
Maja:- NNPP ta amince da tayin Atiku

Jam’iyyar NNPP ta yi maraba da kiran da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi na dunkulewar manyan jam’iyyun adawa don kwato mulki daga jam’iyyar APC mai mulki.
NNPP ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Shugaban jam’iyyar na kasa, Abba Kawu Ali, ya yi ranar Talata a Abuja.
Ali ya ce, “A kwanakin baya ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya yi kira ga manyan jam’iyyun adawa da su hade kai a matsayin hanyar da za a bi wajen ganin an dakile mulkin kama-kamarya da jam’iyyar APC mai mulki ke yi da kuma wanzar da Dimokuradiyya a kasar.
“Jam’iyyar NNPP tana ganin wannan kira na Alhaji Atiku Abubakar a matsayin kishin kasa kuma abin farin ciki ne wanda hakan yasa muke ganin wannan a wani mataki mai amfanarwa,” inji wani bangare daga cikin sanarwar.

-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai3 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi4 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya1 year ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Nishadi4 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano