Connect with us

Hangen Dala

Atiku na son Kara gabatar da shaida a gaban kotun koli

Published

on

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya buƙaci kotun ƙolin ƙasar ta ba shi damar miƙa sabbin hujjoji a ci gaba da matakinsa na ƙalubalantar nasarar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

 

Wata buƙata da lauyoyinsa suka gabatar, ta ce sabuwar shaidar da Atiku ke son gabatar wa kotun za ta tabbatar da zargin da yake yi kan cewa shugaba Tinubu ya yi amfani da takardun bogi a lokacin da yake ƙoƙarin ganin ya fafata a zaɓen shugaban ƙasa.

 

Atiku Abubakar ya ce wannan abu da Tinubu ya yi na nuna cewa ya aikata laifuka biyu, wato ƙirƙirar takardar kammala karatu ta bogi da kuma ƙarya.

 

A cewar Atiku waɗannan hujjoji sun ishi kotun ƙoli ta dogara da su wajen sauke shugaban ƙasar.

 

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar na so ne kotu ta ba shi wannan dama domin ya miƙa mata takardun shaidar kammala karatun Bola Ahmed Tinubu, waɗanda jami’ar jihar Chicago da ke Amurka ta miƙa masa a ranar biyu ga watan Oktoba.

Bayanai dai sun nuna cewa Atiku ya shigar da buƙatar tasa ce a ranar Juma’ar da ta gabata.

 

Sai dai har yanzu kotun ba ta sa ranar da za ta yanke hukunci kan buƙatar ta Atiku ba.

 

Shi dai Atiku Abubakar yana ƙalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu ne ya samu a zaɓen shugaban kasa da aka gabatar cikin watan Fabarairun 2023.

 

A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar Tinubu tare da yin watsi da hujjojin Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na jam’iyyar LP.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Trending