Hangen Dala
Gwamnan Kano ya Sanya hannu Kan kasafin kudi

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a Kwarya-kwaryan kasafin kudin na shekarar 2023 wanda ya kai biliyan hamsin da takwas, da miliyan dari da casa’in da daya, da dubu dari biyar da talatin da biyar, da naira goma sha takwas da kobo goma sha biyu (N58, 191, 535, 018.12), Inda ya zama doka.
Yayin da yake sanya hannu a kasafin kudin, Alh. Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa al’ummar jihar Kano cewa gwamnatinsa za ta bi ka’idojin amfani da kasafin kudi domin kudaden da aka ware za a yi amfani da su ta hanyar da ta dace.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban Sakataren yada labaran gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar.
“Wannan karin kasafin kudin an yi shi ne domin samar da ababen more rayuwa da kasafin kudin shekarar 2023 bai kula da su ba, don biyan bukatun al’ummar jihar Kano.” Gwamnan ya bayyana.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yaba da kokarin kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi bisa yadda suka gaggauta aiwatar da aikin hada daftarin kasafin kudin har aka mika shi ga majalisar dokokin jiha.
Tun da farko, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Jibrin Ismail Falgore wanda ya jagoranci shugabannin majalisar da kuma yan kwamitin kasafi na majalisar ya gabatar da kundin kasafin da majalisar ta amince da shi ga gwamnan domin Sanya masa hannu don ya zama doka a gidan gwamnatin Kano.
Gwamnan ya kuma bukaci ci gaba da samun goyon baya da kyakyawar alaka tsakanin bangaren zartarwa da na majalisar dokoki a jihar Kano.

Baba Suda
Hukumar tattara kudaden shiga ta Kano ta rufe wasu bankuna

Hukumar Tattara kudaden shiga ta jahar kano ta kulle bakin Eco da Zenith dake kan titin Murtala Muhammad. Sakamakon rashin biyan haraji.
Cikakken labarin na Zuwa….

Baba Suda
Kisan Makurdi:- Gwamnatin Kano za ta tura wakilai

Gwamnatin Jihar Kano tayi Allah wadai da kisan mutane biyu Yan Jihar a garin Makurdi dake Jihar Benue.
Cikin sanarwar da Daraktan Gwamnan Kano kan harkokin yada labarai Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ruwaito Gwamnan na Mika sakon jaje ga alummar Jihar da iyalai da ‘yan uwan wadanda abin ya rutsa dasu, Barhma Suleman da Jamilu Ahmad.
Kazalika Gwamnan yayi alkawarin daukar Matakin da ya dace kan batun, tare da fadin gwamnatin Kano za ta tashi wakilai har Zuwa Jihar Benue domin tabbatar da daukar Matakin da ya dace.

Baba Suda
NNPP:- Kwankwaso ya sulhunta rikicin jamiyyar

Rahotanni daga Abuja sun tabbatar da jagoran kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi wani zama da Dan majalisar tarayya Mai wakiltar kananan hukumomin Rimin Gado, Tofa da Dawakin Tofa, Wato Honorable Abdulkadir Jobe, da kuma Daraktan yada labaran Gwamnan Kano Honorable Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ganawar wadda ta gudana a yammacin wannan Alhamis ta kawo karshen Jan Zaren dake faruwa tsakanin Dan majalisar da kuma Sunusi Bature.
A baya bayan nan dai an kai ruwa rana tsakanin su, Inda kowa ne bangare ke mayar da martani.
Abdulkadir Jobe da kuma Sunusi Bature dukkanin su mabiya jamiyyar NNPP ne tsagin kwankwasiyya.

-
Nishadi6 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai5 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai5 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai5 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su