Connect with us

Daurin Boye

Muna da wadataccen Mai – NNPCL

Published

on

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL, ya gargadi jama’ar kasar da su kiyayi sayen mai suna adanawa, don tsoron fuskantar karanci da karin farashin man.

 

Wannan gargadi ya biyo bayan karuwar jerin motoci ne a gidajen mai a sassan kasar a ‘yan kwanakin nan.

 

NNPC Limited, ya ce yin gargadin ya zama wajibi, bisa la’akari da yadda aka fara ganin layukan ababen hawa a gidajen mai a birnin Ikko, cibiyar kasuwancin kasar, da birnin tarayya Abuja da dai sauran wasu garuruwa na Najeriyar.

 

Wata sanarwa da kamfanin man ya fitar, ta ba wa ‘yan Najeriya tabbaci, cewa an gano bakin zaren dangane da abin da ya haddasa layukan ababen hawa a gidajen man.

 

NNPCL, ya ce abin da ya janyo wannan matsala shi ne raguwar dakon man daga ma’ajiyarsa da ke Apapa a birnin Ikko, wato Legas.

 

Amma yanzu haka akwai isasshen mai a adane, wanda aka yi amanna za a kwashe tsawon kwana talatin ana amfani da shi a kasar, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

 

Saboda haka, kamfanin man na Najeriya ya yi gargadin cewa, jama’a su guji sayen man suna adanawa, bisa tsoron za a yi fama da karancinsa.

 

NNPCL, ya ce, nan da ‘yan kwanaki kadan komai zai daidaita game da safararsa zuwa sassan kasar.

 

Ana fatan wannan sanarwa da kamfanin man ya bayar, za ta kwantar wa jama’ar kasar hankali, ta kuma kawar da duk wata fargabar da ake yi, cewa mai yiwuwa an hau hanyar fama da karancin man, ko kuma an fara take-taken da za a kara farashinsa.

Daurin Boye

Zan shiga kawancen ‘yan jamiyyar hamayya – tsohon Minista

Published

on

Tsohon ministan sufurin Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce a shirye yake don shiga ƙawancen ƴan jamiyyar hamayya domin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027

A wata hira da BBC, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce suna ƙoƙarin samar da haɗakar siyasar da za ta samar da sauyi a ƙasar.

Amaechi wanda ɗan jam’iyyar APC ne  ya nuna damuwa kan abin da ya ƙira halin ƙuncin rayuwa da ƙasar ke ciki.

Amaechi ya ce bai cire tsammanin yin takarar shugaban ƙasa ba, illa lokaci ne kawai zai tantance.

Continue Reading

Daurin Boye

Mun kafa kwamiti domin rage farashin – Gwamnatin tarayya

Published

on

Gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zaiyi Duba kan hanyoyin shigo da abinci domin rage farashin sa da kaso 50.

Kwamitin dai dake karkashin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima zai yi aiki ne da wasu ministoci, domin ganin an wadatar Nigeria da abinci.

 

Yayin jawabin sa, Sanata Kashim Shettima yace hakan wani bangare NE na kara inganta tattalin arziki da shugaban kasa Asuwaju Bola Tinubu ke kokari.

 

Continue Reading

Daurin Boye

EFCC ta kwace fasfo din tsohuwar ministar jin kai

Published

on

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC), ta kwace fasfo din tsohuwar Ministar aJin-kai, Betta Edu da magabaciyarta, Sadiya Umar-Farouq, kan binciken badakalar da ake yi a ma’aikatar.

 

Wata majiya mai tushe daga EFCC ta ce an kwace fasfo din Edu da da Sadiya ne domin hana su fita daga Najeriya yayin da ake ci gaba da binciken.

Hukumar ta kwace fasfo din tsofaffin ministocin biyu, Sadiya Umar-Farouq da Betta Edu.

“Mun kuma kwace fasfo din Halima Shehu har sai an kammala bincike. Hukumar ba ta son yin kasadar ganin ko daya daga cikinsu ya fice daga Najeriya alhalin ana bincike a kan su,” in ji majiyar.

Dangane da binciken Edu da Sadiya Umar-Farouq, EFCC ta gayyaci shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz ofishinta a ranar Talata.

Ita ma Halima Shehu, wacce aka dakatar daga hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasa, EFCC na bincike a kan ta.

Continue Reading

Trending