Connect with us

Manyan Labarai

Koyi da halayen Manzon Allah shine mafita a halin da muke ciki, Malam Hafiz Abdullah

Published

on

Fitaccen mai yabon nan Malam Hafiz Abdallah, ya ce koyi da halaye da ɗabi’un Manzon All S.A.W shine mafita daga halin da al’umma suka samu kan su a halin yanzu.

Hafiz Abdallah ya bayyana hakan ne yayin taron maulidin da Dala FM ta gabatar da yammacin jiya Laraba, a harabar gidan dake unguwar Sharaɗa.

Ya ce akwai buƙatar al’umma su ƙara yin koyi da kyawawan ɗabi’un Ma’aiki Annabi Muhammadu S.A.W, da kuma ƙoƙari wajen kula da haƙƙin maƙotaka.

Da yake jawabi yayin taron maulidin amadadin hukumar gudanarwa ta Gungun Gidajen Freedom Rediyo shugaban Gidan Rediyon Dala FM Ahmad Garzali Yakubu, ya bayana godiya ga waɗanda suka halarci taron maulidin.

A nasa jawabin sarkin sharifan Gwale, Sharif Bello Ahmad Banyo, ya ce nuna murnar samun shugaban halitta shaidace ta nuna soyayya ga shugaba Annabi Muhammadu S.A.W.

An dai fara gudanar da maulidin ne tun a shekarar 2016 wanda a wannan shekarar ma ya samu halartal Baki da ma’aikatan Gidan Rediyon Dala FM da na Freedom Radio dake nan Kano.

Manyan Labarai

Uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a Kano sun rasu

Published

on

Rahotanni da dumi-ɗumin sa na bayyana cewar yanzu haka uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.

Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, da tsakar ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.

Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.

Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun kama matashin da ya kunnawa mutane sama da 20 Wuta a cikin wani masallaci – Ƴan Sandan Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da cinnawa wasu mutane Wuta, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubar yau Laraba, a cikin wani Masallaci a garin Larabawar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a yau Laraba, ya ce bayan samun rahoton faruwar al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an su inda suka kai ɗaukin gaggawa.

Matashin da ake zargin mai suna Shari’u Abubakar ɗan shekaru shekaru 38, ya ce shine ya siyo Fetur ya kunna wutar inda ya wurgata a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone a sassan jikin su.

“Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wutar a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.

Koyawa, ya kuma ce daga binciken farko da suka fara matashin ya tabbatar da cewa shine ya sayo Mai a gidan Mai a cikin wata roba, yazo ya kunna wutar, biyo bayan wani rikicin gado da a tsakanin sa da wasu daga cikin mutanen yankin su, inda shima hannayen sa biyu suka ƙone.

Continue Reading

Manyan Labarai

Sama da mutane 20 ne suka ƙone a sassan jikin su bayan da ake zargin wani abu ya fashe a cikin wani masallaci da ke Kano

Published

on

Rahotanni na nuni da cewa an yi zargin fashewar wani abu da asubahin wannan rana ta Laraba, a garin larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a jihar kano, wanda kuma ya jikkata sama da mutane 20, sakamakon ƙonuwa a sassan jikinsu.

Yanzyu haka dai da yawa daga cikinsu sun fara karɓar agajin
gaggwa a babban asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, da ke Kano, kamar yadda wani ganau ya shaidawa
gidan rediyon Dala FM, lokacin da ya ziyarci asibitin a safiyar wannan
rana.

Sai dai wani da ya tsallake rijiya da baya mai suna Yusuf Abdullahi, ya ce yana cikin masallacin lokacin da lamarin ya faru suna tsaka da Sallah Asuba aka kunna wutar daga waje inda aka cillota cikin masallacin, saɓanin abin fashewar da wasu suke faɗa.

Ya kuma ce, “Allah ne kawai ya bani ikon fita Amma mutane da yawa ciki har da yan uwana guda biyu lamarin ya rutsa da su, kuma wutar ta yi musu illa babba saboda ko kasan mutum wallahi idan ka gan shi wallahi ba za ka iya gane shi ba”. Inji Yusuf Abdullahi”.

Wakilin Dala FM, Ibrahim Abdullahi Soron Ɗinki, ya tuntuɓi mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta wayar tarho, sai dai ya ce yanzu haka
yana kan aikin tattara bayanai akan al’amarin, wanda rundunar
za ta fitar nan gaba kaɗan.

Continue Reading

Trending