Connect with us

Hangen Dala

Kotu ta tabbatar da nasarar Fintiri

Published

on

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa ta tabbatar da zaben Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben gwamnan da aka yi aranar 18 ga watan Maris, 2023.

 

Dala FM ta ruwaito cewa bayan zaben gwamnan jihar Adamawa, wanda ya kai ga sake kada kuri’a wanda ya jawo cece-kuce, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana gwamna Fintiri mai ci, wanda ya nemi tazarce a matsayin wanda ya lashe zaben.

 

A zaben da aka sake gudanarwa a watan Afrilu, Fintiri na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861, inda ya doke Aisha ‘Binani’ Dahiru ta jam’iyyar APC wadda ta samu kuri’u 398,738.

 

Binani da wasu ’yan takara sun kai karar kotu suna neman a soke nasarar Fintiri, amma kotun a ranar Asabar ta tabbatar da nasarar gwamna mai ci a karo na biyu.

 

Idan za a tuna dakataccen Kwamishinan Zabe na Jihar (REC), Hudu Yunusa-Ari, ya bar baya da kura bayan kammala zaben da aka yi a ranar 15 ga Afrilu, 2023, lokacin da ya bayyana ‘Binani’ a matsayin wacce ta lashe zaben.

 

Lamarin da ya sanya INEC ta soke hukuncin Yunusa-Ari tare da dakatar da shi yayin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

 

Daga nan ne INEC ta kammala zaben kuma ta sanar da Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara a zaben da aka sake gudanarwa.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Trending