Connect with us

Hangen Dala

Jawabin Atiku na yau litinin

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya nemi gaggauta yi wa tsarin mulkin kasar gyaran fuska don hana duk wata kotu abin da ya kira “boyewa a bayan ka’idojin shigar da kara da musun karya wajen tabbatar da zaben sata da kuma yin zagon kasa ga zaben al’umma”.

 

Atiku Abubakar ya kuma ce dole ne a mayar da zabe da tattara sakamakon zabe ta hanyar laturoni su zama tilas a Najeriya.

 

Wannan wani bangare ne na taron manema labarai da shugaban adawar, kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023, ya gabatar ranar Litinin a Abuja. Taron na zuwa ne kwana uku bayan hukuncin kotun koli da ta yi watsi da shari’arsa na kalubalantar nasarar shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.

 

Atiku ya ce matsayin Kotun Koli ko da yake, shi ne karshe amma dai ya bar baya da kura mai yawa.

 

 

Jagoran adawar na Najeriya ya bukaci bullo da tsarin wa’adin mulki daya na tsawon shekara shida kawai a kasar, wanda ya ce zai riga zagayawa tsakanin shiyyoyin Najeriya guda shida.

 

A cewarsa, hakan zai rage neman mulki ido rufe daga shugabannin da ke kan karagar mulki da kuma raba musu hankali.

 

Sannan matakin a cewar Atiku zai inganta tsarin raba daidai da kuma hadin kan kasa a Najeriya.

 

Haka kuma zai hana wasu shiyyoyi guda biyu ko fiye yin taron dangi suna musayar kujerar shugaban kasa a tsakaninsu ta hanyar mayar da sauran saniyar ware.

 

Karin shawarwarin da Atiku Abubakar ya bayar su ne dora wa hukumar zabe ta Najeriya, alhakin tantance takardun da ‘yan takara da jam’iyyunsu suka gabatar, kuma idan ta gaza yin haka, mai yiwuwa saboda hukumomin da aikin ya rataya a wuyansu ba su yi ba, wajibi ne ta bayyana wa jama’a.

 

Atiku ya ce shawarar na cikin muhimman gyaran fuska da aka gabatar wa gwamnatin mulkin soja wadda ta shirya Babban Taron Tsarin Mulki na Kasa kafin mayar da Najeriya kan tafarkin dimokradiyya.

 

Atiku Abubakar ya ce ba zai taba ja da baya a kan gwagwarmayar da ya faro ba.

 

Ya ce matukar yana raye zai ci gaba da gwagwarmaya tare da ‘yan Najeriya a kan “kyautata dimokradiyyarmu da tsarin aiki da doka da kuma sake fasalin siyasa da tattalin arziki” da Najeriya ke bukata don cimma hakikanin bunkasar arzikinta.

Hangen Dala

Take hakki:- Matakin Amnesty game da kama wasu ‘yan jarida a Kano

Published

on

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Amnesty International, ta yi ala-wadai da cin zarafin ‘yan jarida biyu a Kano, wato mawallafin jaridar kano Times, Buhari Abba da kuma Isma’il Auwal.

Cikin sanarwar sa Ƙungiyar ta wallafa a shafin ta na facebook,
ta ce babu shakka abin da rundunar ‘Yansandan jihar Kano ta yi bisa umarnin Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Ibrahim Waiya abin takaici ne.

Rundunar ‘Yansandan jihar Kano dai ta gayyaci Buhari Abba zuwa sashin binciken manyan laifuka (CID) ne, harma kuma ta tsare shi na tsawon awanni.

Kuma dai ana tuhumar mutanen biyun ne da zargin ɓata sunan kwamishinan, ta hanyar wani ra’ayi da jaridar ta wallafa wanda Isma’il Auwal ya rubuta.

Kungiyar ta Amnesty ta ce duk ba zata lamunci duk wani yunƙuri na takewa waɗannan ‘Yan jarida haƙƙinsu ba.

A ƙarshe ƙungiyar taja hankalin gwamantin kano da kuma rundunar ‘Yansandan jihar, da su guji yunƙurin daƙile ‘yancin faɗin albarkacin baki.

Continue Reading

Baba Suda

Gwamnatin Kano ta musanta labarin da ke cewa za ta saka kafar Wando daya da Sojojin Baka

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin da ke yawo na cewa za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishinan yada labaran jihar Kwamred Ibrahim Waiya shi ne ya bayyana hakan lokacin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da kafafen yada labarai NBC ta shirya a yau Alhamis.

 

Yace gwamnatin Kano za ta hada kai da Yan siyasa masu magana a Rediyo da aka fi Sani da Sojojin Baka, domin tsaftace harkokin siyasar Kano.

 

Haka kuma kwamishinan ya musanta labarin da ke cewa Gwamnatin Kano za ta saka kafar wando daya da Sojojin Baka.

 

Kwamishina Waiya ya kuma ce za su hada kai da kafafen yada labarai domin Kara kawo tsafta a harkokin siyasar Kano.

Continue Reading

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Trending