Connect with us

Hangen Dala

Gwamnatin Kano ta ja hankalin al’umma Kan hukuncin da kotun daukaka Kara za ta yanke

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu gabanin hukuncin kotun daukaka kara da za a yanke a gobe Juma’a.

 

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye, ya raba wa manema labarai a Kano a ranar Alhamis, ta hannun Sani Abba Yola, Daraktan ayyuka na musamman na ma’aikatar.

 

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar su guji tada tarzoma ko kalaman da za su tada hankali kafin da kuma bayan hukuncin kotun.

 

Dantiye, wanda ke mayar da martani kan hukuncin zaben gwamna da za a yi gobe da kotun daukaka kara a Abuja, ya jaddada bukatar jama’a su wanzar da zaman lafiya domin ci gaban jihar da kasa baki daya.

 

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su zage damtse wajen ganin an tabbatar da doka da oda don tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.

Hangen Dala

An gurfanar na Ramat a gaban kotu

Published

on

Wasu yan jam,iyyar NNPP anan kano sun shigar da karar wani tsohon shugaban karamar hukuma.

Mutanen dai sun yi karar hon Abdullahi Garba Ramat tsohon shugaban karamar hukumar Ungogo, a gaban babbar kotun shariar muslinci ta birni.

Masu karar suna zargin Ramat da laifin tayar da hankalin al,imma ta hantar gayyato wasu yandaba suka tare musu hanya a lokacin yakin neman zabe sai dai Ramat din ya musanta zargin.

Mai sharia Ibrahim Sarki Yola ya aike da su wajen yansanda don a fadada bincike.

Alhaji Abubakar Iliyasu shine jagoran masu karar ya bayyana mana matsayarsu

Yanzu haka yansandan shahuci sun bukaci masu kara da su kawo gamsassun hujjoji akan da,awarsu.

Continue Reading

Hangen Dala

An kuma:- shugabannin kananan hukumomi uku sun koma jam’iyyar NNPP

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya karɓi shugabannin ƙananan hukumomi su 3 zuwa jam’iyyar NNPP da suka fito daga APC, sun haɗar da na Nasarawa Auwalu Lawan Shu’aihu Aranfosu, Sai na Garin Malam Mudassir Aliyu da kuma na Dawakin Tofa Hon Ado Tambai kwai, inda gwamnan yace zasuyi aiki tare domin kawowa jihar Kano ci gaba.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan da yammacin Asabar yayin da yake karɓar su a fadar gwamnatin Kano da sauran kansilolin ƙananan hukumomin.

Gwamna Yusuf ya kuma ce a shirye gwamnatin sa take domin karɓar duk wani da yake da kishin al’umma domin ciyar da jihar kano gaba.

Da suke jawabi shugabannin ƙananan hukumomin yayin karɓar tasu sun ce zasu kasance masu bawa gwamnati haɗin kai.

Gwamna Abba yace yanzu haka dukkan shugabannin ƙananan hukumomin da suka dawo za’a dunga gudanar da taron jam’iyya tare da su domin suma sun zama ƴan jam’iyya.

Continue Reading

Hangen Dala

Kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halattaccen gwamnan Kano

Published

on

Kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halattaccen gwamnan kano.

 

Continue Reading

Trending