Kasuwanci
Muna bukatar tallafin gwamnati – me Gyaran Babur
Wani mai sana’ar gyaran Babura a sabon titin Fanshekara mai suna Idris Adamu unguwar Kwari, ya ce tallafawa masu irin sana’arsu daga bangaren gwamnati zai taimaka musu musamman ma da yanzu wasu masu sana’ar suka fara barin ta da ita saboda halin rayuwa.
Idris Adamu ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakilinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, yana mai cewa yadda wasu masu babura suke siyar da ababen hawansu yasa basu fiya samun gyara ba, inda yace idan har gwamnatin zata rinka tallafa musu ta hanyar basu horo da kuma basu kayan aiki, babu makawa hakan zai taimawa sana’arsu ta gyaran Baburan.
Ya kuma ce yanzu haka ta kai ga idan mutum ya kawo babur dinsa, mai-makon yace ayi masa gyara sai yace a nemi mai saye, wanda hakan koma baya ne ga sana’arsu.
Kasuwanci
Da sana’ar siyar da Awara a bakin Titi na sayi Fili, na gina Gida, kuma nake shirin yin Aure a Kano – Mai lalurar Kafa
Wani matashi mai lalurar Kafa da ya rungumi sana’ar siyar da Awara a gefen titin Madobi mai suna Yusif Ibrahim mazaunin Damfami dake karamar hukumar Kumbotso ya shawarci Matasa da su tashi tsaye wajen riko da kananan sana’o’i domin su dogara da kansu.
Matashin mai lalurar kafar ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakikinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, yana mai cewa riko da sana’ar na taimakawa mutum ya dogara da kansa, tare da magance wasu matsaloli da suke damunsu na yau da kullum.
“Sana’ar siyar da Awarar da nake yi da ita na sayi Fili, na gina Gida, yanzu haka kuma ina shirin yin Aure; Ina ganin budi dan haka akwai bukatar sauran matasa su nemi abin yi ko da sana’ar siyar da Awara ne, “in ji shi”.
Matashin ya kara da cewa akwai kalubale a sana’ar amma dai nasarorin sun fi yawa.
Kasuwanci
Rashin tallafa mana na kawo nakasu a sana’ar mu – Masu yafin kayan lambu
Sakatariyar kungiyar mata masu sana’ar yafin Iraruwan kayan lambu na yankin garin Ali dake karamar hukumar Garko Kubra Hassan, ta ce tallafawa masu yafin irin da abubuwan da suka sawwaka, zai taimaka musu wajen wadata kasar nan da kayan lambu ba sai an shigo da su daga kasashen ketare ba.
Kubra Hassan ta bayyana hakan ne yayin zantawarta da wakilinmu na ‘yan Zazu Hassan Mamuda Ya’u, tana mai cewa yanzu haka mata sun rungumi aikin yafin iraruwan kayan lambun, amma rashin tallafa musu daga bangaren gwamnati shine babban kalubalensu wanda hakan kan kawo musu koma baya a sana’ar tasu.
“Mata ku tashi tsaye wajen rungumar kananan sana’o i domin ku dogara da kan su, tare da taimakawa kanku da ma mazajenku a gidan aure, “in ji Kubra,”
Kubra Hassan ta kuma kara da cewa, babban burinsu shine wadata kasar nan da kayan lambu mai-makon ace an dogara da na kasashen ketare.
Kasuwanci
Rashin taimaka mana yana kawo mana koma baya a Kano – Manoman Tafarnuwa
Wani manomin Tafarnuwa dake garin Kofa a karamar hukumar Bebeji mai suna Bala Abdullahi Kofa, ya ce rashin samun tallafi a sana’arsu ta noman Tafarnuwa daga gwamnati kan kawo musu koma baya.
Mallam Bala Abdullahi ya bayyana hakan ne yayin zanatawarsa da wakilinmu Usaini Abdullahi Kofa a ranar Litinin, yana mai cewa matukar gwamnati ta shigo wajen tallafa musu da Taki, da samar musu da Famfon Burtsatse, babu makawa hakan zai kara bunkasa sana’ar tasu ta Noman Tafarnuwar.
Da yake nasa jawabin shima wani Manomin Tafarnuwar mai suna mallam Dalha Labaran Kofa, ya ce karin kalubalen da suke fuskanta a harkar noman Tafarnuwar shine yadda take konewa idan sun dasa ta, biyo bayan rashin wadataccen Taki da sauran matsaloli, inda suke neman daukin mahukunta.
Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da manoma da dama ke kara neman tallafin mahukunta, domin kara bunkasa sana’arsu ta Noma a gurare daban-daban.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su