Connect with us

Siyasa

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa zai sanya baki don hana Shoprite barin Kano

Published

on

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, zai sanya baki don dakatar da yunkurin da katafaren shagon hada-hadar kasuwanci na Shoprite ya ɗauka na rufe reshensa daya tilo a jihar Kano, nan gaba kadan.

Bayanin hakan ya fito nw ta cikin wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar, inda ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan kan al’amarin a Abuja.

Idan dai ba’a manta na katafaren kantin sayar da kayayyakin dake Ado Bayero Mall a Kano, a makon da ya gabata ne suka sanar da matakin ficewa daga cibiyar kasuwanci a watan Janairun da zai kama, inda suka ce hakan ya biyo bayan yanayi na kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu.

Akan al’amarin dai an samu ra’ayoyi daban-daban dangane da matakin da Shoprite zai dauka na tashi daga Kano tun watan Maris na 2014.

Sanarwar ta kara da cewa ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawan ya tanadi tsari mai kyau don dakatar da Shoprite daga dakatar da kasuwanci a Jihar Kano, kuma zai gana da mahukuntan kamfanin a wannan makon inda za a tattauna batun da fatan shawo kan lamarin.

‘’Duk da batun kasuwanci ne tsantsa, amma za mu ga abin da za mu iya yi don karfafa musu gwiwa su janye yunƙurin da suka yanke kuma su cigaba da kasuwanci a Kano. Kamar yadda kowa ya sani, akwai dimbin damammakin kasuwanci a Kano, cibiyar kasuwanci ce ta Arewacin Najeriya. A lokacin da muke zawarcin masu saka hannun jari, ba za mu nade hannayenmu mu kyale su su tafi ba,” inji shi.

Hangen Dala

Lauyoyin gwamnatin Kano sun bukaci a kamo Ganduje

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 7 karkashin jagorancin mai sharia Amina Adamu ta sanya karfe biyu da rabi na ranar yau dan bayyana matsayarta akan batun gurfanar da tsohon gwamnan kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa da wasu mutane.

A zaman kotun na yau lauyoyin gwamnatin jaha sun bayyana wa kotun cewa an sadar da sammace ga wadanda ake kara ta hanyar kafafen yada labarai kamar yadda kotun ta yi umarni tun a baya amma wadanda ake kara basu samu damar halartar kotun ba dan haka ya roki ko dai a kamo su ko kuma kotun ta ci gaba duk da cewar basa gaban kotun.

Sai dai lauyan wanda ake kara na 6 barrister Nuraini Jimo SAN ya yi suka inda ya bayyana cewar kotun ta dakata tun da sun daukaka kara ya kuma bayyana cewar kotun bata da hurumi sannan kunshin tuhume-tuhumen yana dauke ta kura-kurai.

Kotun zata bayyana matsayarta a yau da rana.

Tun da farko gwamnatin kano ta yi karar Ganduje da mutane 6 bisa zargin almundahana akan kudi sama da Naira Biliyan 4 da aka yi zargin sun sayarda wasu filaye sun raba kudin.

Continue Reading

Labarai

Da Dumi Dumi:- EL Rufai ya kai karar majalisar dokoki

Published

on

Tsohon Gwamna jahar Kaduna Mal. Nasir elrufai ya Maka majalisar Dokokin jahar Kaduna a gaban Kotu a bisa bata Masa Suna da majalisar tayi na cewa Gwamnatin sa ta sace kudaden jahar da Suka naura naira miliyan dubu Dari Hudu.

Tsohon Gwamna ya shigar da karar ce, a Gaban babbar kotun taraiyya dake NDA Kaduna a safiyar Laraban nan 26 ga watan Yuni 2024.

Inda ya bukaci Kotun data tursasa majalisar ta bashi hakuri a bainar jama’a, sakamakon Kazafin da Yan majalisan Suka yi masa da mukarraban Gwamnatinsa data gabata.

 

Karin bayani na nan tafe….

Continue Reading

Siyasa

Zauren jam’iyyun haɗin kan kasa IPAC sun cire shugaban jam’iyyar LP na Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su 

Published

on

Sakataren zauren jam’iyyun haɗin kan kasar nan, IPAC na ƙasa reshen jihar Kano, kuma shugaban jam’iyyar APM na Kano Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire shugaban jam’iyyar LP na jihar Kano Abdullahi Raji daga cikin tafiyar su ta IPAC, baki ɗaya.

Sakataren na IPAC, Nuhu Idris ya ce sun dauki wannan mataki ne bisa yadda Rajin ke amfani da kungiyar CUPP, da rusassun jam’iyyun kasar nan suka samar a baya, a dan haka, duk wata jam’iyyar dake da rijista a yanzu na ƙarƙashin IPAC.

Ya kuma ce dokar da ta kafa IPAC, ba ta bai wa ɗan kowacce jam’iyya damar shiga hurumin wata jam’iyyar ba kamar yadda Rajin ke ƙoƙarin yi a rikicin dake faruwa a jam’iyyar APC a nan jihar Kano.

Shugaban jam’iyyar APM, ɗin Honarable Nuhu Idris, ya ce sun cire Rajin daga tafiyar ta IPAC ne, sakamakon wata sanarwa da ya fitar, ya ce, ka da hukumar zaɓe INEC, ta yi watsi da shugaban mazaɓar Ganduje, wanda hakan ba dai-dai ba ne a dokance, dan haka, suka fitar da shi daga cikin tafiyar tare da sanar da shugabancin jam’iyyar sa na kasa.

Continue Reading

Trending