Connect with us

Hangen Dala

Abba da Gawuna:- Yau Alhamis kotun koli za ta fara sauraro

Published

on

Yau Alhamis kotun koli za ta fara sauraron karar da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar NNPP suka daukaka zuwa gaban ta, inda suke kalubalantar nasarar hukuncin kotun daukaka kara da ta baiwa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC nasara.

Tun da fari dai jam’iyyar APC ce ta fara shigar da kara gaban kotun sauraron korafin zabe, inda take kalubalantar nasarar Abba Kabir Yusuf, kuma kotun ta baiwa APCn nasara, hakan ya sanya gwamna Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar NNPP suka daukaka kara zuwa kotun daukaka karar inda nan ma kotun ta sake baiwa Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC, wanda Abba Kabir Yusuf da jam’iyyar NNPP suka garzaya gaban kotun koli tare da kalubalantar wancan hukunci.

A yau Alhamis ne dai kotun ta koli za ta fara sauraron shari’ar, kafin daga bisani ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci.

Hankula dai sun karkata wajen ganin yadda za ta kaya a zaman na yau, musamman korafin jam’iyyar NNPP da ma na jam’iyyar APC dake kalubalantar gaba dayan jam’iyyar NNPP wato ( Cross appeal ).

Abba Kabir Yusuf dai ya samu nasara a zaben 18 ga watan Maris da kuri’u sama da miliyan daya da dubu dari da goma sha tara, inda ya kayar da abokin karawar sa Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya samu kuri’u dubu dari tara da casa’in da wani abu.

Koda dai kotun karbar korafin zabe ( Tribunal ) ta soke kuri’ar NNPP dubu dari da sittin da shida bisa rashin sanya hannu da kuma tambarin hukumar zabe.

 

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Hangen Dala

Gaya Ajingi Albasu:- Dan majalisa ya raba kayan abinci

Published

on

Dan majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu Dakta Ghali Mustafa Fanda ya fara rabon tallafin kayan abinci ga al’ummar kananan hukumomin uku.

 

Yayin rabon tallafin kayan abincin, Dakta Ghali Mustafa yace yayi rabon tallafin ne domin fara sauke nauyin al’ummar da yake wakilta.

 

” Wannan tallafi zamu bayar da shi ne domin fara sauke nauyin al’ummar da suka zabe mu, kuma wannan shi ne karon farko, kuma yayi daidai da bukatar al’umma a yanzu, shiyasa muka fara da tallafin kayan abinci”.

 

“A cikin wannan tallafi mutane kimanin dubu ashirin ne zasu amfana, wanda zamu bayar da buhunan Shinkafa da Gero da Garin masara.”

 

Haka kuma ɗan majalisar ya bayar da tallafin Naira miliyan ashirin ga matasan kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu.

 

Sai kuma ɓangaren dalibai mata, wanda shima a yau dan majalisar ya dauki nauyin karatun dalibai mata guda 60 a bangaren lafiya.

 

Haka kuma cikin jawabin nasa Hon Ghali ya kuma ce nan gaba kadan zai bayar da tallafin taki ga manoma, da kuma farfaɗo da dukkanin rijiyon burtsatse na kananan hukumomin Gaya, Ajingi da Albasu a wani mataki na samar da ruwan sha.

 

Da yake nasa jawabin mataimakin gwamnan Kano Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya samu wakilcin mai baiwa Gwamna Shawara kan harkokin siyasa Hon Sunusi Surajo Kwankwaso kira yayi ga sauran wakilan al’umma da suyi koyi da Dakta Ghali Mustafa Fanda wajen ayyukan alkhairi da kuma jin kan al’umma.

 

Haka kuma Hon Sunusi Surajo ya yabawa dan majalisar bisa bayar da tallafin ga ƙananan hukumomin uku.

 

Taron dai wanda ya gudana a cikin Islamic Centre na karamar hukumar Gaya ya samu halartar manya, da kuma jagororin yankunan uku, kuma nan take Dan majalisar Tarayya Dakta Ghali Mustafa ya fara rabon tallafin

Continue Reading

Hangen Dala

Shugaban kasa ya bayar da umarnin bude Boda

Published

on

Shugaban kasa Asuwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarnin bude iyakokin kasar nan.

Cikin sanarwar da ya fitar shugaban ya ce duk wata iyaka dake tsakanin Nigeria da jamhuriyar Nijar a gaggauta bude ta.

Karin bayani na nan tafe…

Continue Reading

Trending