Connect with us

Addini

Ku dai na nuna halin ko in kula da karatun ya’yanku – Dagacin Dorayi

Published

on

Dagacin garin Dorayi karama dake karamar hukumar Gwale Alhaji Umar Shehu Sani, ya ce kamata yayi iyaye da mawadata su kara himma wajen tallafawa makarantun ya’yansu, ta yadda ya’yan zasu samu ingantaccen ilmi.

Dagacin ya bayyana hakan ne yayin bikin saukar karatun Al-kur’ani mai girma na dalibai masu biye 18, masu hadda kuma ma 18, da makarantar Salafussale dake unguwar Dorayi karama ta gudanar karo na 6, ranar Lahadin din nan, a makarantar ‘yan mata ta Chiranci dake karamar hukumar Kumbotso.Alhaji Umar Shehu ya kuma kara da cewar, bai kamata a iyaye da mawadatan su rinka nuna halin ko in kula akan karatun ya’yan su ba.A nasa jawabin shugaban makarantar ta Salafussale Mallam Ibrahim Abdullahi Bunkure, ya ce abinda suka sa a gaba shine gyaruwar tarbiyyar dalibai, ta yadda daliban zasu zama ababen koyi a tsakanin al’umma.

A cewarsa, “Daliban da kuka yi saukar karatun Al-kur’ani mai girma ku tabbata yanzu ku ka sanya d’an ba wajen neman ilmi ba wai kun kammala ba ne, “in ji shi”.Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar iyayen daliban makarantar Abubakar Lawan Magashi, ya ce za suyi duk mai yiyuwa wajen magance kalubale da matsalolin da makarantar ke fuskanta.

Wakilinmu Hassan Mamuda Ya’u ya rawaito cewa a yayin bikin saukar al’umma da dama ne suka samu damar halarta daga sassan Kano daban-daban.

Addini

Matsin Rayuwa: Shugabanni ku sassautawa al’umma – Babban Limamin Kano

Published

on

Babban limamin Kano, kuma wanda ya jagoranci sallar idi a babban masallacin idin na Kofar Mata a nan Kano, Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, ya ja hankalin shugabanni da su sassautawa al’umma, sakamakon halin matsin rayuwar da ake ciki a yanzu.

Farfesa Muhammed Sani Zaharaddin, yayi jan hankalin ne yayin huɗubar da ya gabatar, bayan kammala sallar idi da ta gudana a yau Laraba, a babban masallacin idin dake unguwar Kofar Mata a Kano.

Ya kara da cewa kasancewar al’umma na cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa, akwai buƙatar shugabanni su yi bakin ƙoƙarin su, domin kawo sauki daga halin matsin halin rayuwar da ake fama dashi.

Yayin sallar Idin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da sauran al’umma da dama ne suka halarta.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Abba Haruna Idris ya rawaito cewa, Farfesa Muhammed Sani ya kuma ja hankalin al’umma, da su koma ga Allah Subhanahu wata’ala domin samun dacewa a Duniya da gobe Ƙiyama.

Continue Reading

Addini

Ku fara duban watan Sallah daga gobe Litinin – Fadar Sarkin Musulmi

Published

on

Yanzu haka kwamitin ganin wata na Fadar mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al’ummar musulmin ƙasar nan da su fara duban jinjirin watan Shawwal, daga gobe Litinin, 8 ga watan Afrilun, 2024 da ake ciki.

Bayanin hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a yammacin yau Lahadi a jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce, duk wanda ya ga watan Shawwal, ya sanarwa Mai Gari ko Hakimi mafi kusa wanda kuma zai sanar har zuwa fadar Sarkin Musulmi.

Har ila yau, fadar Sarkin musulmin ta kuma bayar da lambobin waya waɗanda mutane za su yi amfani da su wajen ba da rahoton ganin watan Sallah ga fadar Sarkin musulmin, kamar yadda kafar yaɗa labarai ta BBC ta rawaito.

Continue Reading

Addini

Iyaye ku kula da tarbiyyar ƴaƴan ku – Malama Fatima Tsakuwa

Published

on

Malamar addinin musulunci dake nan Kano Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta shawarci mata da su ƙara himma wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da kuma zaburar da su mahimmancin yin addu’a a cikin wannan wata na Ramadana, domin rabauta da rahamar Ubangiji S.W.T.

Malama Fatima Ahmad Tsakuwa, ta bayyana hakan ne yayin taron bita ta musamman da gidauniyar Bango Charity Foundation ƙarƙashin Malama Fatima Yusif Mai tama, wanda gidauniyar ta shirya wa Mata, da bitar ta shafi watan Azumin Ramadana, akan yadda iyaye matan za su kula da ƴaƴan su, da ya gudana a ofishin ƙungiyar dake unguwar Sharaɗa a Kano.

Wakiliyar tashar Dala FM Kano, ta rawaito cewa malama Fatima Tsakuwa ta ce akwai buƙatar iyayen su ƙara lura da tarbiyyar ƴaƴansu, tare da yawaita karatun Al-kur’ani mai girma domin rabauta da falala a wajen Allah S.W.T.

Continue Reading

Trending