Manyan Labarai
Sabuwar Shekara: Shugaba Tinubu zai yiwa ‘yan kasa jawabi
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu zai yiwa ‘yan kasar jawabi dangane da sabuwar shekara a gobe Litinin 01 ga watan Janairun 2024.
Bayanin hakan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, aka rabawa manema labarai da yammacin Lahadin nan.
Sanarwar ta kuma ce shugaba Tinubu zai gabatar da jawabin nasa ne da misalin karfe 7 na safe a gidan talabijin na Najeriya (NTA) da kuma gidan rediyon tarayyar Najeriya FRCN.
An kuma bukaci sauran kadafen yada labarai da na zamani wato kadafen sada zumunta, su jona ta nan NTA din, da kafar rediyon tarayya FRCN, domin sanar da al’umma shirar ta sa.
Manyan Labarai
Dagatai da masu unguwanni ku guji ɓoye mana bayanan sirri akan ƴan Daba da masu fashin Waya – Rundunar Tsaro a Kano
An buƙaci Dagatai da masu unguwanni da su guji ɓoye bayanan sirri akan ƴan Daba ko ɓata gari a duk lokacin da aka buƙaci sanin hakan dan ɗaukar mataki, domin gujewa abinda kaje ya dawo.
Mashawarci na musamman ga gwamnan Kano akan harkokin tsaro, kuma kwamandan rundunar tsaro masu rajin kawar da masu ƙwace wayoyi, da ɓata gari ta KOSSAP, Inuwa Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan ne a zantwar sa da gidan rediyon Dala FM Kano.
Ya kuma ce matuƙar dagatai da masu unguwannin za su rinƙa ɓoye musu bayanan sirrin a duk lokacin da suka ɓoƙaci sani, babu makawa hakan ka iya haifar da barazana ga rawanin su.
A cewar sa, “Mafi yawan lokuta idan muka je wajen masu unguwanni ko kuma dagatai, neman wani bayanan sirri akan wasu ɓata gari sukan ɓoye mana kuma ba zamu lamunci hakan ba zamu sanar da gwamna abinda ke faruwa, “in ji Inuwa Sharaɗa”
Inuwa Salisu, ya kuma ƙara da cewa a ƙoƙarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, na magance matsalar tsaro a sassan jihar, ya samar da wani haɗakar jami’an tsaro wato Task Force, da za su rinƙa shiga lungu da saƙo, dan ganin tsaro ya inganta tare da kawar da masu fashi da makamin wayoyin mutane.
Inuwa, ya ci gaba da cewa, “Jami’an mu za su ci gaba da hoɓɓasa a ciki da wajen Kano wajen kawar da ɓata garin da suke addabar mutane a faɗin jahar mu; Duk wanda muka kama zai gayawa Aya zaƙin ta, “in ji shi”
Wannan dai na zuwa ne yayin da al’umma ke ci gaba da neman ɗaukin mahukunta wajen magance matsalar tsaro a sassan jihar Kano, da ma ƙasa baki ɗaya.
Manyan Labarai
Uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a Kano sun rasu
Rahotanni da dumi-ɗumin sa na bayyana cewar yanzu haka uku daga cikin mutane sama da 20 da wani matashi ya cinnawa Wuta cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, da tsakar ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.
Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.
Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.
Manyan Labarai
Mun kama matashin da ya kunnawa mutane sama da 20 Wuta a cikin wani masallaci – Ƴan Sandan Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi da ake zargi da cinnawa wasu mutane Wuta, a lokacin da suke tsaka da Sallar Asubar yau Laraba, a cikin wani Masallaci a garin Larabawar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.
Kakakin rundunar ƴan sandan SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwar da ya aikowa Dala FM Kano, a yau Laraba, ya ce bayan samun rahoton faruwar al’amarin ne Kwamishinan ƴan sandan Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tura tawagar jami’an su inda suka kai ɗaukin gaggawa.
Matashin da ake zargin mai suna Shari’u Abubakar ɗan shekaru shekaru 38, ya ce shine ya siyo Fetur ya kunna wutar inda ya wurgata a cikin masallacin, lamarin da ya sa mutane da dama suka ƙone a sassan jikin su.
“Aƙalla mutane 24 ne suka ƙone bayan da matashin ya kunna musu wutar a cikin masallacin, wanda tuni jami’an mu suka kai su asibitin Murtala Muhammad da ke Kano, inda suke ci gaba da samun kulawar likitoci, “in ji SP Kiyawa”.
Koyawa, ya kuma ce daga binciken farko da suka fara matashin ya tabbatar da cewa shine ya sayo Mai a gidan Mai a cikin wata roba, yazo ya kunna wutar, biyo bayan wani rikicin gado da a tsakanin sa da wasu daga cikin mutanen yankin su, inda shima hannayen sa biyu suka ƙone.
-
Nishadi4 years ago
Ina neman mijin aure – Rayya
-
Labarai4 years ago
Hamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Manyan Labarai4 years ago
KAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Nishadi5 years ago
Mansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Labarai4 years ago
Auren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya2 years ago
Rahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai4 years ago
Sabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi5 years ago
An gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su