Connect with us

Manta Sabo

Kisan Ummita: Kotu ta sanya ranar sauraren jawaban karshe kan tuhumar da ake yi wa Frank Geng

Published

on

Babbar kotun jahar Kano mai lamba 17 dake zamanta a unguwar Miller Road, karkashin mai shari’a Justice Sunusi Ado Ma’aji, ta d’age ci gaba da sauraren shari’ar dan kasar Chaina, mai suna Frank Geng Quarong, da ake zargi da kashe tsohuwar budurwarsa tun a ranar 16 ga watan satumba 2022 da ta gabata.

Yayin zaman kotun na ranar Litinin din nan lauyan gwamnatin Kano Barista Ibrahim Arif Garba, ya shaida wa kotun cewar lauyan, wanda ake tuhuma Barista Balarabe Muhammed Dan-Azumi bai basu jawabin karshe ba akan lokaci sai a ranar 27 ga watan Disambar 2023, inda suke ci gaba da yin nazari akansa.

Daga bisani ne dai lauyan gwamnatin jahar Kano, ya roki kotun ta ba su wata rana dan gabatar da jawabin karshe kamar yadda jaridar idongari.ng, ta ruwaito labarin.

Lauyan wanda ake zargi Barista Balarabe Muhammed Dan-Azumi, ya bayyana cewar ya bayar da rubutaccen jawabin karshen tare da hujjojin da yake neman kotun ta saki wanda ake zargi, bisa rashin kwararan hujojji da masu gabatar da kara suka gabatar cewar ya aikata laifin na Kisa.

A karshe dai mai shari’a Justice Sunusi Ado Ma’aji ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 22 ga watan Janairun 2024, dan bangarorin shari’ar su gabatar da jawaban su na karshe a shari’ar.

Manta Sabo

Wata Kotu a Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar da aka shigar da ƙaramar hukumar Gwale da wani mutum

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 15 da ke zamanta a Mila Road a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ta ci gaba da saurarar karar da al’ummar unguwar Dorayi Baba unguwar jakada suka shigar da karamar hukumar Gwale, da wani mutun mai suna Alhaji Ibrahim Ƴan Shana.

Tunda fari dai mutanan unguwar sun shigar da karar ne suna zargin karamar hukumar ta Gwale, da cefanar wa Ibrahim ‘yan Shana wani fili mallakin al’ummar unguwar na makaranta, lamarin da su garzaya gaban kotun tun a shekarar 2023, a lokacin shugabancin ƙaramar hukumar da ya shuɗe, suna rokon da ta dawo musu da shi domin a gida makaranta a yankin nasu.

Sai dai a zaman kotun na yau bangaren wadanda ake kara na daya wato karamar hukumar Gwale sun gaza gabatar da martanin su akan karar, inda suka roki kotun da ta sanya wata ranar domin gabatar da martanin nasu.

Wakilimmu Mu’az Musa Ibrahim ya rawaito cewa mai shari’ar ya sanya ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2024 domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Manta Sabo

Kotu ta aike da matashin da ake zargi da kashe matar sa gidan yari a Kano

Published

on

Kotun majistret mai lamba 29 karkashin jagorancin mai Shari’a Talatu Makama, ta aike da wani matashi gidan gyaran hali.

Matashin mai suna Adamu Ibrahim ana zargin sa ne da laifin hallaka mai ɗakinsa ta hanyar kwantara mata dutsen Guga, a fuskarta a can garin kwanar ɗan gora.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar, tun a ranar 9 ga watan 4, wani mai suna Idris Adamu yaje caji ofishin ƴan sanda inda ya shigar da kara akan cewar Adamu Ibrahim ya kashe mai ɗakinsa wadda kuma kanwa ce a wajen mai ƙarar Idris Adamu.

Bayan fitowa daga kotun ne wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’ila, ya zanta wanda ake zargi wanda ya ce tsautsayinya sanya shi aikata hakan.

Shima dan uwan marigayiyar ya bayyana matsayarsu, inda ya roƙi kotun da ta yi musu adalci a shari’ar.

Kotun dai ta sanya ranar 17 ga watan gobe dan a kara gabatar da shi a gaban ta domin ci gaba da shari’ar.

Continue Reading

Hangen Dala

Yau za’a fara Shari’ar Ganduje da gwamnatin Kano

Published

on

A yau ne babbar kotun jaha mai lamba 4 zata fara sauraron wata sharia wadda gwamnatin kano ta ahigar.

 

Gwamnatin jahar kano dai ta shigar da karar tsohon gwamnan jahar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat Umar Ganduje da kuma dansu Umar Abdullahi Ganduje da kuma wani kamfani mai suna Lamash da kuma Dr Jibrilla Muhammad.

 

Gwamnatin jahar kano dai tana zargin Ganduje da wadanna mutane da laifin hada baki da barnatar da dukiyoyin gwamnati.

 

 

Cikin zarge-zargen da ake yiwa su Ganduje akwai batun sun sayar da wasu filotai ba bisa ka’ida ba.

 

 

Da kuma batun zargin da akewa Ganduje na badakalar karbar dala tun a shekarar 2019.

 

 

Yanzu haka an girke jami,an tsaro a harabar sakateriyar Audu Bako inda kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci kotun zata fara sauraron korafin kamar yadda wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito

Continue Reading

Trending