Manyan Labarai
INEC ta soke zaben cike gurbi a karamar hukumar Kunci dake Kano
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta dakatar da zaben cike gurbi a karamar hukumar Kunci dake jihar, biyo bayan yadda aka samu wasu bata gari da suka fasa akwatuna tare da hana zaben.
Kwamishinan hukumar zaben na jihar Kano Ambasada Abdu Zango ne ya bayyana hakan yayin zantawarsa da manema labarai da yammacin Asabar din nan, ya ce bayan fasa akwatunan zaben da ‘yan ta’addan suka yi, tare da rakiyar jami’an tsaro suka je suka taho da ma’aikatansu da kuma taho da kayan da suka rage.
Abdu Zango ya ce daga cikin tsattsauran matakin da hukumar zaben ta kasa INEC, ta dauka har da dakatar da zaben a karamar hukumar ta Kunci, sai kuma wani lokacin.
Manyan Labarai
Babu ɗaga ƙafa tsakanin mu da duk wanda ya take haƙƙin mutane a Nijeriya – Human Rights
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Sustainable Growth initiatives for Human Rights Development, ta ce babu ɗaga ƙafa a tsakanin ta da dukkanin wanda ya take wa wasu haƙƙi a Nijeriya, tana mai cewa za ta yi duk mai yiyuwa don ganin an dawo wa da dukkan wanda aka cuta haƙƙinsa.
Daraktan ƙungiyar na ƙasa Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ne ya bayyana hakan yayin zantwar sa da gidan rediyon Dala FM Kano, jim kaɗan bayan da su ka buɗe sabon ofishin ƙungiyar reshen unguwar Ƴanshana da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, ranar Lahadi 09 ga watan Nuwamba, 2025, a Kano

Kwamared Abubakar, ya kuma ce za su ci gaba da hoɓɓasa wajen ganin sun ci gaba da bibiya akan cutar da aka yi wa mutane, don ganin an ƙwato musu haƙƙoƙin da aka danne musu ba tare da gajiya wa ba.

A cewar sa, “Daga cikin kuɗirin mu har da nema wa Matasa ayyukan yi, don yaƙi da rikice-rikicen faɗan Daba, da ƙwacen Wayoyi, da kuma daƙile shaye-shayen kayan maye a tsakanin al’umma, tare da taimakon marayu, don inganta rayuwar su, in ji Abubakar.”

Da yake nasa jawabin, sabon shugaban ƙungiyar ta Sustainable Growth initiatives for Human Rights and Development, reshen unguwar Ƴanshana da ke ƙaramar hukumar Kumbotso a Kano, Kwamared Yunusa Muhammad Ahmad, ya ce a shirye su ke wajen ci gaba da bibiya tare da kare haƙƙin bil’adama.

A yayin taron, an ƙaddamar da shugabannin da za su jagorancin aikin ƙungiyar na sabon ofishin da aka buɗe, wanda Kwamared Yunusa Muhammad Ahmad, zai jagorance su.

Taron ya samu halartar al’umma da dama, kuma ciki har da limamin masallacin unguwar Ƴanshana Mallam Muhktar, da mai unguwar yankin, da kuma kwamandan ƙungiyar sintirin Bijilante na unguwar, da dai sauransu.
Manyan Labarai
Kotu ta sanya ranar yanke wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci
Yanzu haka Babbar kotun Tarayya da ke birnin Abuja, ta saka ranar 20 ga watan Nuwamban 2025, domin yanke wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu hukunci akan tuhumar da ake yi masa.
Mai shari’a, a kotun, James Omotosho, ne ya bayyana haka a zaman kotun na ranar Juma’a 07 ga watan Nuwamba, 2025, a kan shari’ar da ake yi wa Kanu kan zargin ta’addanci.
Maishari’a James, ya ɗauki matakin ne bayan da Nnamdi Kanu, ya kasa fara kare kansa bayan kwana shida da kotun ta ba shi domin yin hakan, kamar yadda kafar BBC ta ruwaito.
Har ila yau, kotun ta kuma ce bayan Kanu ya gaza amfani da damar da aka ba shi domin kare kansa daga tuhumar da ake yi amsa, bai kamata ya ci gaba da iƙirarin da yake yi cewa an hana damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na jin bahasinsa.
Idan ba a manta ba, a ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne dai, kotun ta ɗage zamanta domin bai wa wanda ake ƙara damar kare kansa kamar yadda ya buƙata a baya, sai dai a yanzu ya kasa kare kan nasa.
Manyan Labarai
Kotu ta yanke wa magidanci hukuncin sharar Masallaci na tsawon wata 6 a Kano
Kotun shari’ar Musulunci mai lamba daya da ke zamanta a Kofar Kudu, ta yanke wa wani magidanci hukuncin share Masallacin Wudilawa na tsawon wata shida bayan samun sa da laifin dukan matarsa.
Tunda fari, matar ta garzaya Ofishin ‘yan sanda ne da ke Jakara a Kano, inda ta yi ƙarar mijinta cewar ya doka mata Muciya a kanta sakamakon haka har sai da ta yi jinya.
Bayan Jin korafinta ne aka turasu Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba daya da ke Kofar Kudu karkashin jagorancin mai sharia Shamsuddin Ado Abdullahi Unguwar Gini.
An kuma gurfanar da shi a kotun, bisa tuhumar samar da rauni, kuma bayan karanto masa ya amsa laifinsa, amma lauyansa wato daya daga cikin lauyan taimakon marasa ƙarfi Barista Muhammad Ali Tijjani, ya roƙi ayi masa sassauci.
Hakan ya sa kotu ta amince, ta kuma yanke masa hukuncin ɗaurin talala, inda zai share masallacin Wudilawa na tsawon watanni shida a sati sau uku.
Haka kuma, an tsalala masa bulala goma, kuma an umarcr shi da ya biya matar kudin maganin da ta kashe wato Naira dubu goma, kamar yadda Freedom Radio ta ruwaito.

-
Nishadi6 years agoIna neman mijin aure – Rayya
-
Labarai5 years agoHamisu Breaker ya kai kan sa wajen ‘yan sanda
-
Nishadi6 years agoMansura Isah ta yi kaca-kaca da Sadiya Haruna
-
Manyan Labarai6 years agoKAROTA: An baiwa Baffa Babba wa’adin kwanaki bakwai
-
Labarai6 years agoAuren dan Panshekara da ba Amurkiya ya samu cikas
-
Lafiya3 years agoRahoto: An gano wani gida da ake gini da takardun Kur’ani da Alluna
-
Manyan Labarai6 years agoSabuwar damfarar da ta fito a Kano
-
Nishadi6 years agoAn gano daliban da Adam Zango ya dauki nauyin karatun su
