Connect with us

Manyan Labarai

Ba ‘yan kungiyar mu ne suka kashe Abba Dan Snake ba a Kano – Kungiyar Bijilante

Published

on

Kungiyar sintirin bijilante ta kasa reshen jihar Kano karkashin kwamandan ta Ubale Barau Muhammad Badawa, ta ce ba jami’anta ne suka yi sanadiyyar rasuwar matashin nan dan unguwar kofar Na’isa mai suna Abba Dan Snake ba.

Jami’in hulda da jama’a na kungiyar a matakin jahar Kano, kuma kwamandan ta na karamar hukumar Fagge, Usman Muhammad Dan-Daji, ne ya bayyana hakan ga gidan rediyon Dala FM da safiyar Litinin din nan, ya ce mutanen da ake zargi da kashe matashin kusan sama da kwanaki 170, ba jami’ansu ba ne, ‘yan kwamitin unguwa ne.

A ranar Asabar ne dai aka gano gawar matashin Abba Dan Snake a cikin wani kududdufi dake yankin Hauren Shanu, bayan da aka shafe kusan kwanaki 170, da kashe shi, inda wasu mutane da wasu kafafen yada labarai suka rinka bayyana kungiyar Bijilante a matsayin wadanda suka kashe shi a lokacin, lamarin da kungiyar ta musanta.

Daga bisani dai kungiyar Bijilanten ta gargadi wadanda ba ‘yan kungiyarsu ba ne suke kuma sanya irin kakinsu da su dai na domin gujewa abinda ka je ya zo, kasancewar irinsu ne suke bata musu suna.

Usman Dan-daji, ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, da hukumomin tsaro, ‘yan kungiyoyin kare hakkin dan adam, da lauyoyi, da shiga cikin al’amarin don daukar mataki ga ‘yan kwamiti da kuma wasu ‘yan kunguyoyi da ake samu suna daukar doka a hannu, da har take kaiwa ana rasa rayuka.

Manyan Labarai

Zamu farfaɗo da masana’antun ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano – Kwamishina

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta farfaɗo da masana’antun yin saƙa na ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar nan, domin samawa matasa aiki ta yadda za su dogara da kansu.

Kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ne ya bayyana hakan, yayin da ya ziyarci masana’antar saƙar kayayyaki ta ƙaramar hukumar Kura yau Laraba, domin duba halin da take ciki tare da duba yadda za’a farfaɗo da ita daga dogon suman da ta yi.

Tun dai a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a shekarar 2014, ne ya samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin Kano da ta ganata ta yi watsi da masana’anatar.

Yayin duba masana’antar Kwamishinan cikinki da masana’antu na jihar Kano Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya kuma bada tabbacin farfaɗo da masana’antar yin saƙar ta ƙaramar hukumar Kura da ma na faɗin jihar nan, domin samawa matasa ayyukan yi.

Da yake yiwa Dala FM Kano, ƙarin bayani babban sakataren ma’aikatar ciniki da masana’antu na jihar Kano, Muhammad Yusuf Ɗan-duwa, ya ce, farfaɗo da masana’antar ta Kura, na zuwa ne bisa ƙokarin gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, domin samawa matasa ayyukan yi.

Ya kuma ce yadda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da masana’antar tsawon lokaci, a yanzu gwamnatin su za ta yi duk mai yiyuwa, domin ganin an ta ci gaba da aiki ka’in da na’in.

Tun dai a shekarar 2014 ne aka samar da injina a masana’antar, amma tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta wofantar da aikin, lamarin da ya sa aikin ya tsaya cak, inda gwamnatin Kano mai ci a yanzu ta ce za ta farfaɗo da ita domin samawa matasa aikin yi, da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Mun ware miliyoyin Kuɗi domin biyan ƴan Fansho haƙƙoƙin su – Gwamnan Kano

Published

on

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatin sa ta ware Naira biliyan biyar domin biyan ƴan Fansho haƙƙoƙin su bisa la’akari da yadda ake samun matsala wajen biyan su kudaɗen su.

Gwamnan Kano ya yi wannan jawabin ne da safiyar yau Laraba, yayin taron majalisar zartarwa da gwamnatin jihar ta saba yi duk sati, domin tattauna batutuwan da suka shafi gwamnatin jihar Kano.

“Za mu tabbatar an biya dukkanin waɗanda suka dace hakkin su na Fansho, domin su samu damar gudanar da sana’o’in dogaro da kai da za su iya riƙe iyalan su, “in ji Gwamnan”.

Wakilinmu na fadar gwamnatin Kano Umar Abdullahi Sheka ya rawaito cewa, gwamnatin Kano ta ce za ta tabbatar ta magance matsalar rashin ruwa da al’umma suke fuskanta a sassan jihar, domin samar musu da wani sauƙi.

Continue Reading

Manyan Labarai

Kotu ta zartas da hukuncin hallasta yarjejeniyar ƴan kasuwar Sabon Gari da hukumar gudanarwar kasuwar

Published

on

Babbar kotun jaha mai lamba 1, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta zartas da hukunci a kunshin wata ƙara wadda Alhaji Musa Yakubu da mutane 7 suka shigar, suna ƙarar hukumar kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi wato Sabon Gari da shugaban hukumar.

Tunda farko, masu karar sun garzaya gaban kotun ne domin neman kotun ta tabbatar da yarjejeniyar da ke tsakanin ƴan kasuwar da hukumar kasuwar.

Masu ƙarar sun bayyana wa kotun cewar, tun a zamanin mulkin Soja suka ƙulla yarjejeniya da hukumar kasuwar a kan za su gina shaguna a filin kasuwar, kuma za su saɓunta biyan haraji bayan shekaru 15, masu ƙarar sun bayyana cewar kafin shekaru 15 din su cika hukumar kasuwa ta karɓe shagunan.

Da take zartas da hukuncin mai Shari’a Dije Aboki Aboki, ta ayyana cewar wannan yarjejeniya da ke tsakanin kungiyar ƴan kasuwar da hukumar kasuwar halastacciya ce kuma kotun ta tabbatar da ita.

A zaman dai mai Shari’a Dije Aboki ta halastawa ƴan kasuwar ta Sabon Gari, a ɓangaren Barkono da gidajen wanka a shagunan da suka mallaka a karkaahin waccan yarjejeniyar.

An kuma ayyana cewar hukumar kasuwar Sabon Gari, da shugaban hukumar za su biya Naira dubu dari biyu ga ƴan kasuwar.

Continue Reading

Trending